Uncategorized

Mummunar Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 18 A Babbar Hanyar Legas Zuwa Ibadan

Hukumar kiyaye aukuwar hadura ta kasa (FRSC) ta tabbatar da cewa, mutune 18 ne hatsarin mota ya hallaka a gadar Isara da ke kusa da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Asabar..

Jami’in watsa labarai na FRSC, Bisi Kazeem, ya shaida ta cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi cewa, “Daga rahoton binciken hadarin da ya faru da ya rutsa da motoci guda uku dauke da fasinjoji 25 da suka kunshi maza 6 manya, babbar mace guda, yaro karamin, da wasu mutum 17 da ba iya gano yanayinsu ba sun kone kurmus ba tare da ana iya ganesu ba.

“Daga cikin wannan adadin, mutum 18 sun mutu, sauran bakwai din kuma sun gamu da munanan raunuka da suka hada da manyan maza biyar, babbar mace guda da karamin yaro.”

Ya kara da cewa, binciken ya nuna cewa musabbabin hadarin da ya kunshi motoci kirar Mazda biyu da Previa bus shine gudun wuce sa’a da kuma karya dokokin tuki.

Kazalika, Corps Marshal na FRSC, Dr Boboye Oyeyemi, ya gargadi direbobi da suke kokarin kauce wa tukin dare, tare da jawo hankalinsu da suke bin ka’idojin tuki a kowani lokaci domin kiyaye rayukansu da na fasinjojin da suke dibowa.

Da yake magana dangane da jerin hadarin ababen hawa da suka auku da karfe 10:20 na daren ranar Asabar a kusa da gadar Isara (KM 61-750) da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Leave a Reply