Babu Barakar Siyasa Tsakanina Da Maidalan Misau, Cewar Hon. Bakoji Bobbo


Daga Mohammed Kaka Misau, Bauchi
Hon. Bakoji Aliyu Bobbo, Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, ya bayyana cewa, ko kadan babu wani rashin jituwar da ya barke a tsakaninsa da Ahmed Ibrahim Dandija (Maidalan Misau).

A maimakon haka ma godiya yake yi ga Maidalan Misau a matsayin sa na Uban gidansa tare bayyana wa masu yada jita-jita da gulma kan akwai matsala a tsakanin su da Maidalan Misau.

Ya bayyana Maidalan Misau a matsayin wanda ya saka shi a tafiyar Kaura tun kafin fara yakin neman zaben 2019 wanda ya rike matsayin Daraktan gudanarwa, tsare-tsare da adana na yakin neman zaben sa har zuwa ga nasara, “Muna tare da Maidalan Misau, masu yada gulma don neman abinci su yi tayi amma muna tare dari bisa dari,” a cewarsa.

Hon. Bakoji Aliyu Bobbo wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya halarci taron bikin kaddamar da kungiya mai rajin tallata jami’iyyar PDP gida-gida wato ‘PDP Door-to-Door’ a karamar hukumar Misau tare da fafutukar tabbatar da zarcewan Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Abdulkadir a babban zaben 2023.

A cikin jawabinsa, Shugaban marasa rinjaye na majalisar, ya yaba wa wannan kungiyar bisa wannan yunkuri da suka yi tare da jan hankalin ‘ya’yan kungiyar kan tafiya sawu da kafa da uwar jami’iyya don samun nasara da tabbatar da kudirori na jami’iyya, “Hakan shi ne zai kawo nasara a dukkan abubuwan da aka sanya a gaba. Don a PDP akwai ladabi da da’a da girmama Shugabanci tare mutunta juna”.

Hon. Bobbo ya kara da bukatar mambobin kungiyar da su rike gaskiya da amana, “Kar a sanya son kudi a gaba da komai, a maida hankali wajen hada kan al’umma, idan aka samu akasin haka lalle ba za a samu abun da ake so ba, rashin gaskiya ne ke rushe dukkan wani kudiri da aka dumfari aiwatarwa.”

Ya bayyana jami’iyyar PDP a matsayin jami’iyya mai kokari gurin yin aiki a kasa ba yada jita-jita da karya don samun goyon bayan al’umma ba, yana mai cewa, “Ita siyasa karuwa ce, idan babu karuwa ba ta da amfani, matukar al’umma ba za su amfana da shugabanci ba babu amfanin sa.”

Bakoji Bobbo ya shawarci mambobin kungiyar da su shiga kwararo-kwararo da lunguna domin yayata manufofin PDP da bayyana ayyukan alkhairi da Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad Abdulkadir ya yi a karamar hukumar Misau da jihar Bauchi baki daya.

“Ku yayata ayyukan da mai girma gwamna Bala Muhammad da ya yi mana na hanyar Sade zuwa Akuyam, ya gina mana gidaje sama da dari, yana gyara mana babban asibitin Misau, an gina kananan asibitoci, da sauran su, Duk wadanda abun yadawa ne ga al’umma.

“Yanzu haka ana shirye-shirye tallafawa mutane da masu kananan sana’o’i da jarin da bai yi kasa da naira dubu hamsin (50,000) ga kowanne wanda akalla za a raba kudi da ya kai ga Naira Miliyam Hamsin (50,000,000.00) a karamar hukumar Misau. A cigaba da bada hadin kai ga jami’iyyar PDP da Gwamnatin jihar Bauchi, alkhairai masu yawa suna zuwa In Sha Allahu.”

Minority Leader ya yaba wa Hon. Abubakar Ahmad Garkuwan Misau bisa amince da ya yi na karban takaran Shugaban karamar hukumar Misau don bada gudumawar sa ga al’umma, “Wannan abun alfahari ne a matsayin sa na wanda ya rike babban matsayi na dan majalisar tarayya ya zo yanzu ya rike karamar hukuma don ceto al’umma.”

Ya yi amfani da damar wajen godiya na musamman ga daukacin matasan Misau bisa da’a da yin siyasa cikin tsafta da babu kalare/sare-sare, haka shine abun da akeso ba rigima da zubar da jinin juna don banbancin ra’ayi ko jami’iyya, a fadinsa.

Hon. Bakoji ya yi godiya ga iyayen jami’iyya irin su Alh. Adamu Abdullahi, Alh. Yarima sa’i, Alh. Mukhatari Dambam, Alh. Babayo Akuyam (ABA) Alh. Hamza Koshe Akuyam, da dukkan dattawan jami’iyya bisa shawari da dora shi akan hanya da suke yi Yau da kullum.

Daga karshen Shugaban kungiyar ‘Misau PDP door- TO- Door Initiative And Enlightenment For Kaura 2023 Continuety, ya yi jawaben godiya da kuma bada tabbacin za su yi iya kokarin su gurin tabbatar da wannan kungiya akan tsarin jami’iyyar PDP da biyayya ga Shugabanci.

%d bloggers like this: