DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Goma sha Takwas: Neman daren Lailatul Qadr

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

‘Yan’uwa, wadannan kwanaki goman karshe na Ramadhan da muke cikinsu, a cikinsu dare mai albarka yake, wato daren Lailatul Qadr, daren da Allah ya yi baiwar falalolinsa ma wannar al’umma, kuma ya fifita ta da su a kan sauran al’ummomi.

Daga cikin albarkan daren a cikinsa aka saukar da Alkur’ani, a cikinsa ake raba dukkan lamari na kaddara tabbatacce, ma’ana; a cikinsa Allah yake fayyace duk abin da zai afku a wannan shekara, ya kaddara shi babu canji, daga “Lauhul Mahfuz” zuwa ga Mala’iku marubuta, na kaddaran arziki, da ajali, da alheri da sharri har karshe. Allah ya ce: {Lallai mu mun saukar da shi (Alkur’ani) a dare mai albarka, lallai mun kasance masu gargadi. A cikinsa ake raba dukkan lamari na kaddara tabbatacce} [al-Dukhan: 3-4].
Allah ya siffanta daren da albarka, saboda falalarsa da yawan alheran da suke cikinsa.

Daga cikin albarkan wannan dare na Lailatul Qadr yin ibada a cikinsa ya fi ibada a wata dubu. Allah ya ce: {Mu mun saukar da shi ne (Alkur’ani) a cikin daren Lailatul Qadr. Me ya sanar da kai Lailatul Qadr? Lailatul Qadr ya fi wata dubu. Mala’iku da Ruhi (Jibreel) suna yawan sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu na kowane lamari aka kaddara. Daren aminci ne har zuwa ketowan al-fijr} [al-Qadr: 1-5].

Al-Qadr ma’anarsa girma da daraja da daukaka, ko kuma ma’anarsa ita ce: Kaddara abubuwa da Allah yake yi. An kira daren da wannan suna ne saboda dare ne mai girma da daraja da daukaka, a cikinsa Allah yake kaddara duk abin da zai faru a shekara.

Daren ya fi wata dubu, ma’ana; ya fi su falala da daukaka da yawan lada, shi ya sa duk wanda ya yi Sallar dare a cikinsa yana mai imani da neman lada to za a gafarta masa zunubansa da suka gabata. Kamar yadda ya tabbata daga Annabi (saw) a Hadisin Abu Huraira (ra): Bukhari (1901), Muslim (760).

Saboda girma da darajar wannan dare Mala’iku, tare da shugabansu Mala’ika Jibreel (as) suna yawan saukowa, suna saukowa da al’amuran da Allah ya kaddara.

Kuma dare ne wanda yake cike da aminci ga Muminai, suna da aminci daga dukkan wani abin tsoro, saboda yawan wadanda Allah yake ‘yantawa daga wuta a cikin daren.

Lallai a cikin wannar Sura akwai bayanin falaloli masu yawa na wannan dare, daga cikinsu:

Falala ta farko:
Allah ya saukar da Alkir’ani a cikin daren, littafin da ya kasance shiriya ga mutane, kuma sa’ada gare su a Duniya da Lahira.

Falala ta biyu:
Allah ya girmama sha’anin daren, ta yadda ya yi tambaya a kansa, ya ce: {Me ya sanar da kai daren Lailatul Qadr?}.

Falala ta uku:
Daren ya fi watanni dubu falala da girman matsayi.

Falala ta hudu:
Mala’iku suna yawan sauka, su kuma ba sa yawan sauka sai ga abu mai girma da matsayi da muhimmanci. Kai, har Mala’ika Jebreel (as) shugaban Mala’iku shi ma yana sassaukowa, wanda hakan yake nuna girman matsayin daren.

Falala ta biyar:
Daren aminci ne saboda yawan kubutar bayi daga azaba da uquba, saboda bayi suna yawaita da’a da ibada ma Allah a cikinsa.

Falala ta shida:
Allah ya saukar da Sura ta musamman don bayanin girma da matsayi da daraja da albarka da falalar daren, da alheran da ke cikinsa.

Daga cikin falalolin daren Lailaitul Qadr, duk wanda ya yi Sallar dare a cikinsa yana mai imani da neman lada to an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa, kamar yadda ya tabbata daga Abu Huraira (ra), Annabi (saw) ya ce: ((Duk wanda ya yi Sallar dare a daren Lailatul Qadr, yana mai imani da neman lada to an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa)). Bukhari (1901), Muslim (760).
Abin nufi; wanda zai samu gafaran shi ne wanda ya yi Sallar dare a cikin daren yana mai Imani da Allah, tare da yarda da ladan da Allah ya tanadar wa masu Sallar, kuma yana halin neman lada da sakamako a wajensa.

Daren Lailatul Qadr a cikin watan Ramadhan yake, kamar yadda Allah ya ce: {Mu mun saukar da shi ne (Alkur’ani) a cikin daren Lailatul Qadr}. Kuma ya ce: {Watan Ramadhan wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa shiriya ne ga mutane da bayanin shiriya da rarrabewa}. Baqara (Aya: 185).
Don haka Daren Lailatul Qadr a cikin watan Ramadhan yake, tun da saukar da Alkur’ani ya kasance ne a cikin watan Ramadhan, a cikin daren Lailatul Qadr.

Daren Lailatul Qadr a cikin kwanakin goman karshe na Ramadhan yake, shi ya sa Annabi (saw) ya ce: ((Ku nemi daren Lailatul Qadr a kwanaki goman karshe na Ramadhan)) Bukhari (2020), Muslim (1169).

Kuma a cikin kwanaki goman ma a cikin wutri suke. Wato daren 21, 23, 25, 27, 29. Saboda fadin Annabi (saw): ((Ku nemi daren Lailatul Qadr a wutri, a kwanaki goman karshe na Ramadhan)) Bukhari (2017).

Kuma an fi tsammanin daren a kwanaki bakwai na karshe, saboda ya tabbata daga Ibnu Umar (ra) ya ce: ((Wasu mutane cikin Sahabban Annabi (saw) an nuna musu daren Lailatul Qadr a cikin mafarki, a kwanakin bakwai na karshe, sai Annabi (saw) ya ce: ((Ina ganin mafarkin naku ya dace a cikin kwanaki bakwai na karshe, don haka duk wanda zai nemi daren to ya nema a kwanaki bakwai na karshe)) Bukhari (2015), Muslim (1165).

A cikin kwanaki bakwai din kuma an fi tsammaninsa a cikin daren Ishirin da bakwai, saboda abin da ya tabbata daga Ubayyi bn Ka’ab (ra) ya ce: ((Na rantse da Allah na san wane dare ne (daren Lailatul Qadr), a sanina mai karfi shi ne daren da Manozn Allah ya umurce mu da mu yi Sallah a cikinsa, shi ne daren Ishirin da bakwai)). Muslim (762).

Amma Malamai sun rinjayar da cewa; daren Lailatul Qadr yana canzawa, idan a wannan shekarar ta kasance a daren ishirin da bakwai, to wata shekarar ta yiwu ta kasance a daren ishirin da uku, ko da biyar ko da tara. Shi ya sa Annabi (saw) ya ce: ((Ku nemi daren Lailatul Qadr a cikin kwanaki goman karshe na Ramadhan, a kwanaki tara da suka rage, a kwanaki bakwai da suka rage, a kwanaki biyar da suka rage)) Bukhari (2021).

Allah Madaukakin Sarki ya boye sanin daren ne ga bayi don hikimarsa, da kuma rahmarsa ga bayi, don su dage da Ibada cikin dukkannin kwanaki goma na karshen watan, sai aikinsu na Ibada ya yawaita, ladansu ya yi yawa, su rabauta da yawan ibada; Sallah, Zikiri, Karatun Alkur’ani da Addu’o’i a cikin daren, sai su kara samun kusaci da daukaka a wajen Allah Madaukaki, su samu lada masu yawan gaske.

Kuma ya boye sanin daren ga mutane don yin jarabawa ga bayi, don masu kasala su bayyana daga masu himma da kokarin ibada. Don idan mutum yana neman abu to bai kamata ya zama mai kasala a neman ba, kamata ya yi a ga yana da himma da kokari mai yawa wajen nemansa.

‘Yan’uwa, a cikin daren Lailatul Qadr Allah yana saukar da rahma, yana ‘yanta bayi daga wuta, yana gafarta zunubai, yana rabon falala da arziki da lada mai yawa a kan ibada a cikin daren, ibada a daren ya fi ibada a wata dubu. Ku yi kokari wajen neman wannan alheri da albarka mai yawa mai girman gaske. Kwanaki ne kadan, ku dage a cikinsa kar ku yi kasala.

Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da yawaita aiyukan da’a a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya. Ya sa mu dace da daren Lailatul Qadr.
Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu tsoron Allah da kishin al’umma da tausayin talakawa.

%d bloggers like this: