Uncategorized

HON. BAKOJI ALIYU BOBBO YA AZA TUBALIN GINA BANDAKAI A TSANGAYAR UNGUWAR DUNIYA DA FADI.

By: Mohammed kaka Misau, Bauchi

Dan Majalisan dake wakiltan mazabar Chiroma a majalisar dokokin jihar Bauchi Hon. Bakoji Aliyu Bobbo wanda kuma shine shugaban marasa rinjaye a majalisar ya aza tubalin Gina bandakai a tsangayar Almajirai dake yankin Duniya da Fadi wanda kungiyar ‘Bobbo Youth Mobilization and Initiative Forum bakin Tasha’ ke ginawa.

Dayake jawabi a yayin wannan aiki, Bakoji Bobbo yayi godiya bisa kokari da wannan kungiya keyi gurin tallata ayyukan alkhairin sa, da kuma jajircewa gurin tallata hidimar siyasar ‘Bobbo Political Academy, inda ya bayyana irin nasarori dake samu a matsayin addu’o’i da al’ummah da masoya keyi yau da kullum.

Bakoji Aliyu Bobbo ya kuma nemi al’ummah da magoya bayanshi da su ci gaba da masa addu’o’i na alkhairi da fatan gamawa da Shugabanci lafiya, cikin nasara da mutunci,

Yace “gama Shugabanci ana mutunta Mutum da daraja shi shine abun fata ba ana Allah wadarai ba”. – Inji shugaban marasa rinjaye.

Anashi jawabin, Malamin tsangaya ya bayyana Jin dadin sa tare da gabatar da addu’o’i na Kariya, Jagoranci, nasara da zaman lafiya cikin jam’i tare da dukkan almajirai masu karatu dake wannan tsangaya baki daya.

Shugaban wannan kungiya, Mal. Umar Usman (Jan Wando) a madadin Yayan kungiyar ya bayyana farin cikin su a wannan unguwa bisa hadin kai da nuna damuwa da ‘dan majalisar keyi a dukkan hidima na alummah da suka saka a gaba, harma da dukkan hidima data taso a wannan unguwa a dukkan Lokacin da aka nemi tallafin sa.

Ya kuma Kara bayyana aniyar wannan kungiya Kan cigaba da tsare – tsare da jajircewa gurin tallata nasarori da bayyana alkhairin Hon. Bakoji Aliyu Bobbo a koda yaushe.

Daga karshe al’ummar wannan unguwa sun koka Kan matsalar hanyar shiga da fita na wannan unguwa da suke fama dashi dake bukatar cikon kasa, ‘dan majalisar Bakoji Aliyu Bobbo nan take ya duba wannan guri sannan ya bada umarni za’a fara kaiwa kasan ciko don gyara wannan hanya saboda a samu saukin shiga da fita a wannan unguwa.

Leave a Reply