Nasarar Tsaro: Gwamnan Yobe Ya Dage Takunkumin Hawa Mashina A Potiskum Da Kananan Hukumomi 9

Daga Mohammed Kaka Misau, Bauchi

Labari mai dadi da ke riskomu a yammacin yau Litinin na cewa Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya amince da dawo da hawa babur a wasu kananan hukumomi 10.

Wannan matakin bai rasa nasaba da irin nasara da cigaba da ake samu wajen kyautata harkokin tsaro da yaki da mayakan Boko Haram da suka addabi jihar.

Kananan Hukumomi da dage takunkumin hawa Mashina ya sha sun hada da Fune, Nangere, Potiskum, Fika, Jakusko, Yusufari, Bade, Karasuwa, Nguru da Machina.

Gwamnan wanda ya shelanta hakan a fadar mai martaba Sarki Nguru lokacin da ya je masa jajena gobarar da ta samu wasu ‘yan kasuwa.

Idan za a iya tunawa dai Gwamnatin jihar ta soke hawa Babura ne tun a wata Janairu na shekarar 2012 sakamakon matsalolin tsaro da yadda ake amfani da Mashina wajen kai hare-hare a shekarun baya.

Wasu mazauna yankunan da dage takunkumin ya shafa sun nuna farin cikinsu da cewa hakan zai kara saukaka walwala da jin dadin al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: