Shatiman Misau yayi rabon tallafin Azumi na dubban naira a Misau-Dambam.

Daga : Mohammed kaka Misau

Dan Takaran kujeran Majalisan Wakilai a Mazabar Misau Dambam wato Hon. Sulaiman Yamai Misau kuma Shatiman Misau ya raba katon katon din taliya wa Al’ummar yankinsa na Misau Dambam.

Cikin jawabinsa Hon Sulaiman Yamai Misau yace yayi wannan hubbasa ne ga Al’ummar Yankin domin saukaka musu a cikin wannan wata Mai Alfarma na Ramadan.

Shatiman Misau yace a matsayin sa na Dan Jam’iyyar APC ya raba wassu daga cikin kayayyakin karkashin jam’iyyar APC a inda kowacce karamar hukuma ya bada Katon Katon da dama Na Taliya na “Yayan jam’iyya a hannayen shugaban Jam’iyyar kananan hukumomin.

Ya kara da cewa baya ga Jam’iyya Ya raba wasu katon katon din wa ‘Yan uwa da abokan Arziki gami da wasu daga cikin Al’ummar gari.

Shatiman Misau yace “Naji dadi matuka yadda naga mutane musamman a kafar sadarwa ta zamani suna nuna jin dadin su gami da yabo a gareni, wasu ma har kirana suke a waya suna mun godiya duk da dai ni ban taba rike wata kujerar siyaba, lallai wannan abu nayi ne domin nima na samu lada a cikin wannan wata na ramadan”.

Daga karshe yayi Kira ga shugabanni na jam’iyyar APC Wadanda zasuyi zaben fidda gwani da suyi kokari wajen fidda “Yan takarar da suka dace domin samun nasara a zaben me zuwa na Dubu biyu da ashirin da Uku (2023).

%d bloggers like this: