Uncategorized

Yanzu-yanzu: Gwamnan Bauchi Na Neman Majalisa Ta Amince Da Sabbin Kwamishinoni

Daga Idris Shehu Zarge

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad ya zaba tare da tura jerin sunayen wadanda ya ke son su zama sabbin kwamishinoninsa ga majalisar dokokin Bauchi domin tantance su tare da amincewa.

Idan za ku iya tunawa dai, gwamnan a watannin baya ya dakatar da kwamishinonin jihar gaba daya tare da wasu masu bashi shawara na musamman domin yin garanbawul wa gwamnatinsa.

A wata sanarwar da mai magana da yawun Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abdul Ahmad Burra ya fitar a yau din nan, ya bayyana cewar gwamnan ya turu sunayen ne domin neman tantancewa da amincewar majalisar.

Sanarwar ta ce, wadanda gwamnan ke son su zama masa sabbin kwamishinoni sun hada da, daga Alkaleri ya zabi Abdulkadir Ibrahim; sai karamar hukumar Bauchi: Garba Dahiru; Bauchi: Nuruddeen Abdulhamid; Dambam: Ahmed Aliyu Jalam; Darazo: Dayyabu Chiroma; Dass: Maryam Garba Bagel; Gamawa: Umar Babayo Kesa; Giade: Asma’u Ahmed; Jama’are: Usman Abdulkadir Middibo; Itas – Gadau: Hajara Jibrin Gidado.

Sauran su ne, Katagum: Sama’ila Dahuwa Kaila; Misau: Aminu Hammayo; Shira: Hamisu Muazu Shira; Tafawa Balewa: Sama’ila Burga; Tafawa Balewa: Abubakar Abdulhamid Bununu; Toro: Aliyu Usman Tilde; sai kuma daga karamar hukumar gwamnan ya zabi Warji: Abdulrazak Nuhu Zaki.

Ga fuskokin wasu daga cikin tsoffin kwamishinoni kuma wadanda gwamnan ya aike da sunayensu domin neman amincewar majalisar domin su sake zama sabbin kwamishinoninsa.

Leave a Reply