Yanzu-yanzu: Majalisar Dokokin Zamfara Ta Tsige Mataimakin Gwamna

Yanzu-yanzu: Majalisar Dokokin Zamfara Ta Tsige Mataimakin Gwamna

A yau ne majalisar dokokin jihar Zamfara ta kammala bin matakan tsige mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Mahdi Gusau daga kujerarsa.

Tsige mataimakin gwamnan wanda ya faru a zaman majalisar na yau Labara jimkadan bayan da zauren majalisar ya amshi rahoton kwamitin da babban jojin jihar Justice Kulu Aliyu, ya kafa domin bincike zarge-zargen da ake yi wa Mahdi.

Kwamitin mai mutum bakwai ya gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan, kwamitin a karkashin jagorancin Justice Halidu Soba, ya mika rahoton aikinsa ga majalisar.

Kakakin majalisar dokokin jihar Nasiru Mu’azu shine ya amshi rahoton kwamitin daga hannun Justice Soba.

Daga daga cikin mambobin kwamitin, Oladipo Okpesoyi, ya shaida wa kakakin cewa kwamitin ya gudanar da aikinsa bisa cancanta da dace gami da bin ka’idojin aiki.

Okpesoyi, wanda babban lauya ne mai mukamin SAN ya shaida cewar sun bi dokoki wajen gudanar da aikinsu da tattara shaidun da suka dace kafin kammala aikinsu.

Shi kuma Kakakin majalisar ya sha alwashin bin rahoton kamar yadda kundin tsarin mulki na 1999 ya tanadar.

Mataimakin gwamnan wanda dan jam’iyyar PDP ne an jima ana kai ruwa rana a tsakaninsa da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle.

Leave a Reply

%d bloggers like this: