Takaitattun labaran Safiyar Jumma’a 27/08/2021CE – 18/01/1443AH
An sami karin mutum 835 da suka kamu da cutar Corona a Najeriya, jimilla 189,715.
‘Yan bindiga sun sako daliban kwalejin noma da suka sace a jihar Zamfara.
Sanata Ali Ndume ya nemi Shugaba Buhari ya fito ya yi wa al’umma bayanin halin da ake ciki kan tsaro a Najeriya.
Wata kotu da ke zama a Birnin Kebbi ta dawo da Uche Secondus kan mukaminsa na shugabancin PDP.
Jami’an hukumar kwastam sun mika wasu magunguna marasa rajista da suka kwata a jihar Kaduna ga hukumar NAFDAC.
Gwamnatin jihar Kaduna ta kwashe dalibai yar asalin jihar dake karatu a jami’ar Jos.
Babban sufeton ‘yan sanda ya karbi rahoton kwamitin binciken Abba Kyari.
Shugaba Buhari ya tura dakarun kar-ta-kwana 100 Zamfara domin yaƙar ƴan bindiga.
Kotu ta garkame wasu mutane takwas da ake zargin sun yi garkuwa da matar kwamishinan jihar Benue.
Shugaba Buhari ya ce kamfanin NNPC ya sami ribar Naira bilyan 287 a 2020, karon farko cikin shekaru 44.
Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum bakwai tare da rusa gidaje 74,713 cikin wannan wata na Agusta a fadin jihar.
Wani Magidanci ya rataye kansa bayan kashe matarsa a Bayelsa.
Gobara ta yi sanadiyar fashewar abubuwa a ma’adanar makaman sojojin Kazakistan.
Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta soke ziyarar da za ta kai Isra’ila.
Manchester City ta sayi Christiana Ronaldo daga Juventus a kan kudi yuro milyan 25.
Ku cigaba da kasancewa da mu.