Hausa

Da Dumi-Dumi: Matasa Sun Daka Woson Kayayyaki A Gidan Gwamnatin Bauchi Da Ke Azare

Daga Khalid Idris Doya

Matasan da ke zanga-zangar neman saukin rayuwa sun kutsa kai cikin gidan Gwamnatin jihar Bauchi (masaukin baki) da ke garin Azare shalkwatar karamar hukumar Katagum, gami da gidan tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi Sanata Baba Tela inda suka wawushe komai.

Rahotonni da ke zuwa sun tabbatar da cewa matasan sun shiga wuraren ne a ranar Litinin yayin zanga-zangar matsin rayuwa.

Da ya ke tabbatar ma wakilinmu abun da ya faru, ganau kuma mazaunin Azare, Lukman Azare ya ce, “Yau mun tashi a Azare babu dadi domin an tashi da kone-kone da zanga-zanga.”

“Da y ke ni ina cikin GRA ne unguwarmu dai sun shiga gidan tsohon mataimakin gwamnan sun farfasa sun kwashe kujeru da su AC da duk abubuwan amfani, haka ma suka yi a government lodge inda suka wawushe kayan da ke ciki.”

Kan abubuwan da ke faruwa a cikin garin kuwa ya ce nan ma akwai bayanan abubuwan marar dadi da suka wakana.

Har-ila-yau, akwai rahotonnnin da ke cewa matasan sun je sakatariyar karamar hukumar Katagum domin zanga-zangar ta su sai dai babu tabbacin irin barnar da aka samu a sakatariyar zuwa yanzu.

Kazalika, wakilinmu ya labarto cewa akwai zargin da ke yawo na cewa wani dan sanda ya harbi wani matashi a kofar sakatariyar da ke Azare, shalkwatar karamar hukumar Katagum.

Wakilinmu tuntubi shugaban karamar hukumar Katagum, Malam Musa Azare domin jin ta bakinsa, sai dai bai dauki kiran da aka yi ta masa ba.

Sai dai a cikin kwaryar Bauchi matasa sun fito zanga-zangar amma jami’an tsaro sun dakileta. Sai dai an jibge jami’an tsaro a wurare daban-daban.

Leave a Reply