Hausa

Da Ɗumi-Ɗumi: Masarautar Bauchi Ta Warware Rawanin Sanata Buba Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna Bala

Daga Khalid Idris Doya

Masarautar Bauchi ta sanar da warware rawanin ‘Mujaddadin Bauchi’ da ta naɗa wa Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar bisa sukar gwamna Bala Muhammad.

Idan za a tuna dai a yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen kujerar shugabancin ƙananan hukumomi na jam’iyyar APC, Sanata Buba ya zargi gwamnan jihar Bauchi da jefa jama’a cikin matsin rayuwa inda ya ce gwamnatin jihar ce ke da alhakin ƙuncin rayuwa da ake ciki ba wai shugaba Tinubu ba.

Har ma ya zargi gwamnatin jihar da karɓar tallafin tirelolin shinkafa da taki amma ba ta rabar wa jama’a kamar yadda gwamnatin tarayya ta umarta ba. Sanatan wanda ke ƙoƙarin kare Tinubu daga sukar da gwamna Bala ya masa a kwanakin ba.

A wata wasiƙa daga masarautar Bauchi ɗauke da sanya hannun Nasiru Musa, a madadin Sakataren Majalisar da ya fitar a ranar Laraba, ta nuna abun da ya faru tsakanin gwamnan da Sanata a matsayin rashin biyayya da cin zarafi don haka ne ta cimma matsayar janye ‘Sarautar Mujaddadin Bauchi’.

Wasiƙar wacce aka aike wa Sanatan kai tsaye na cewa, “Bayan gaisuwa da fatan kana lafiya. Bayan haka, a zaman Majalisar Masarautan Bauchi na yau 14/8/2024 ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Bauchi, ta yi nazari mai zurfi kan abubuwan da ya faru na rashin biyayya da cin zarafi wa Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi wanda yin hakan ya saɓa wa irin tarbiya da al’adan Masarautar Bauchi.

“Bisa wannan dalili Majalisa ta janye sarautar da ta baka na Mujaddadin Bauchi.”

Leave a Reply