Hausa

Da Ɗumi-Ɗumi: PDP Ta Lashe Dukkanin Zaɓen Shugabanni Ƙananan Hukumomin Bauchi

Daga Khalid Idris Doya

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC) ta ayyana cewar jam’iyyar PDP da ke mulki a jihar Bauchi ita ce ta lashe dukkanin kujerun zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi na jihar a zaɓen da ya gudana a ranar Asabar.

Zaɓen wanda aka gudanar a gundumomi 323 da suke faɗin jihar da jam’iyyun siyasa guda bakwai suka shiga aka dama da su.

Da ya ke sanar da sakamakon zaɓen a daren ranar Asabar, shugaban hukumar Ahmed Makama, ya ce za su miƙa shaidar lashe zaɓe ga zaɓaɓɓun a ranar Lahadi.

Ya sanar da cewa za a shelanta waɗanda suka lashe zaɓen kansiloli 323 a jihar daga baya, sai dai ya ce jam’iyyun adawa sun samu nasara a kujerar kansiloli 3, yayin da PDP ta lashe dukkanin sauran.

Waɗanda suka kasance zaɓaɓɓun su ne: ƙaramar hukumar Alkaleri Hassan Garba Bajama (shugaba), Abbas Ibrahim (mataimaki); Bauchi Mahmoud Baba Maaji (shugaba), Adamu Muazu Luda (mataimaki); Bogoro – Lawi Yakubu Sumi (shugaba), Markus Masoyi Mulki (mataimaki); Dambam- Yakubu Garba Tela (shugaba), Iliya Isah (mataimaki); Darazo – Sama’ila Yau Sade (shugaba), Amina Musa (mataimaki); Dass – Muhammad Abubakar Jiboa matsayin shugaba yayin da aka zabi Isah Abdulmumini Hanakuka a matsayin mataimakin sa; Gamawa Madaki Ahmed Gololo shugaba Umar Yakubu (mataimaki); Ganjuwa Mohammed Idris Miya (shugaba), Saleh Ahmed (mataimaki).

Sauran su ne: Giade Usman Muhammad Saleh (shugaba) Bahijja Auwalu (mataimaki); Itas Gadau -Hajara Jibrin Gidado (shugaba), Shuaibu Ahmad (mataimaki); Jama’are -Hon. Inuwa Abdullahi (shugaba), Saleh Muhammad (mataimaki); Katagum – Yusuf Babayo Zaki (shugaba), Misbahu Ibrahim (mataimaki) Kirfi – Abdulkadir Umar Dewu (shugaba), Mohammed Mohammed Bashir (deputy); Misau – Salisu Hussaini (shugaba); Moh’d Garba (mataimaki).

Sauran kuma su ne Ningi – Nasiru Zakarai (shugaba), Isah Mohammad (mataimaki); Shira – Abdullahi Ibrahim Beli (shugaba) Adamu Usman (mataimaki); T/ Balewa – Sama’ila Wakili Lere (shugaba), Maigari Ahmed (mataimaki); Toro -Pharm. Ibrahim Abubakar Dembo (shugaba), Adamu Umar Danyaro (mataimaki); Warji – Aminu Barmini (chairman), Habib Idris Usman (mataimaki), yayin da kuma Zaki – Adamu Yakubu (shugaba) da mataimakinsa Ibrahim Chiroma.

Leave a Reply