Uncategorized

Ra’ayi: Raddi Ga Tsohon Wakilin Birnin Bauchi


KARE BAI GAJI ABIN KIRKI BA, IDAN YA YI MA DUKAN SA AKE YI  (I)
Tare da Lawal Muazu
Wani wawa ne da ya shafe tsawon lokaci yana fama da tabin hankali, ana haka sai azumin watan Ramalana ya zo, daya, biyu har ashirin da tara ranar duba watan sallah, al’ummar Annabi suka fara duba wata a sararin samaniya, shi kuwa gogan naka ya je gefe ya tsaya. 
“La ga shi can, ga shi can” Inji wawa lokacin da yake kiran jama’a su zo su ga wata. 
Yuuu! Aka dunguma sai wajen wawa. “Ina watan?” Jama’a suka tambaya. Wawa ya daga kai sama, ya juya, ya juyo. 
“La ga wani watan ma ta Gabas,” inji wawa lokacin da jama’a suke duba yamma. 
Jama’a suka ce ashe bai warke ba, a mayar shi turu! 
Bayan shafe shekaru biyu da watanni da dan majalisar dokoki ta tarayya mai wakiltar Bauchi, Yakubu Shehu Abdullahi (tubabben Wakilin Birnin Bauchi) ba tare da tsinana komai wa al’ummar da yake jagoranta a Abujan ba, baya ga hidimar dawakai da azurta kai da babatu, wakilin a yanzu ya dauko sabon salon neman suna domin fakewa don rufe zunuban sa a idon al’ummar Bauchi. 
Jihar Bauchi karkashin jagorancin Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ta samu cigaba a fannoni daban-daban na rayuwa duk da karancin kudaden shiga da rashin samun cikakken goyon baya da hadin kai daga yawancin ‘yan majalisun dokoki na tarayya har ma da Sanatoci. 
Kadan daga cikin masu mukamai a birnin tarayya ke hada kai da gwamnatin jiha don tallafawa al’ummar Bauchi la’akari da halin kuncin rayuwa da ake ciki a yau. 
Ayyukan wakilin Bauchi a majalisar dokoki ta tarayya sun hada da azurta kai, ta da husuma, wasan tseren doki, izgili baya ga raina manya da iyayen Kasa. 
Idan har wasu ‘yan majalisu na ayyukan tallafawa al’ummar su a sassa daban -daban cikin wannan wa’adin mulki, menene ayyukan Wakilin Bauchi?
Kodayake tsintacciyar mage ba ta mai, amma mutane da dama sun yi tunanin samun sauyi da nadamar rayuwa daga wakili lura da hanyar da ta kawo shi wannan kujera wato tsananin rabo da kuma rashin katabus na gwamnatin da ta shude. 
Cikin wani faifayin bidiyo da tsohon wakili birni ya fito a cikin kwanakin nan yana nuna yatsa ga maigirma gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad inda ya yi zargin wai ana basa barazanar kisa baya ga tozarta jihar Bauchi da Wakili ya yi a wannan babatu, ya kuma ya tuna al’uma wani tsohon zargin kisa da aka taba yi wa wani mutum anan Bauchi inda gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) suka yi ta yayatawa shekarun baya. 
Wakili kamar wani dan majalisar dokoki anan jiha da jaridu suka ruwaito cewa ya karkatar da wata hanya zuwa wani Otel mallakar sa, shi ma ya yi nasarar azurta kai da dukiyar al’ummar da yake wakilta wajen sayen dawakai na alfarma domin burge kansa. 
Gwamna Bala Muhammad ba shi da lokacin biyewa ‘yan adawa domin inganta jihar Bauchi ta hanyar cika alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe kadai ya saka a gaba.
Shin dan majalisa yana tunanin babatu ne abinda aka zabe shi yayi ko yana tunanin al’u.mar Bauchi ba ta waye ba ne?.


Tuntuni Bauchi ta waye kuma salon siyasar yau ba ta kai jahili ya mulki masu ilimi ba, kuma babu wanda zai buya a laifin sa ya buya cikin tawagar sari-ka-noke.
Ban yi wannan raddi da Ingilishi ba domin turancin ungulu gane shi sai sarkin fawa! 
Lawal Muazu Bauchi Mai tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yada labarai na zamani Talata 7, Satumba 2021.

6 thoughts on “Ra’ayi: Raddi Ga Tsohon Wakilin Birnin Bauchi

Leave a Reply