Uncategorized

Dan Takarar Majalisa Ya Nemo Tallafin Naira 20m Don Gina Masallaci Da Makaranta A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya

Dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Bauchi a mazabar Toro/Jama’a karkashin lemar jam’iyyar NNPP, Ibrahim Garba Tilde ya nemo tallafin naira miliyan ashirin wa kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’ah Wa Iqamatussunnah (JIBWIS) reshen Tilden Fulani da ke karamar hukumar Toro domin sayen filin gina masallacin Idi da makaranta.

Da ya ke mika kudin ga kungiyar, Ibrahim Garba ya shaida cewar hakan na cikin kokarinsa na nemo cigaba ga al’ummar mazabar, ya kuma ce, ya nemo tallafin kudade da wasu tallafin ga al’ummarsu daga wajen abokan kasuwancinsa da abokansa wanda a bisa haka ne ma daya daga cikinsu ya bada wannan kudaden ta hannunsa.

Ya ce, tallafin an nemo ne domin kungiyar ta samu mallakar filin Idi na dindindin tare da samun damar karasa makarantar da ake ginawa a harin Tilde.

A cewar dan takarar, wanda ya bada tallafin ba ya son a bayyana sunansa amma ya yi hakan ne domin Allah don ya taimaka tare da yin fatan za su yi amfani da kudade ta hanyoyi da suka dace domin cigaban addinin musulunci.

Ibrahim Tilde ya bai wa kungiyar da al’ummar mazabarsa tabbacin cewa baya ga gyaran fanfunan tuka-tuka guda 100 da ya yi, zai cigaba da jawo hankalin masu tallafi domin su kawo tallafinsu wannan yankin.

Ya ce, dukka wadannan somin tabi ne domin idan ya samu damar zama dan Majalisa zai tabbatar ya kyautata rayuwar al’ummar mazabarsa.

Da ya ke amsar kudaden a madadin kungiyar, Shugaban kungiyar JIBWIS reshen Tilde, Malam Abdullahi Muhammad, ya nuna matukar godiyarsu bisa hakan tare da tabbatar da cewa za a yi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace.

Ya ce, kungiyar a wannan matakin bata taba amsar maguden kudade a matsayin tallafi, don haka ya mika godiyarsu kan hakan tare da addu’ar Allah saka ma wanda ya yi wannan tallafin da alkairi gami da wanda ya nemo.

Ya misalta Ibrahim Tilde a matsayin mai hidima wa addini kuma dan da ya nuna soyayya da kauna ga al’ummarsa, ta ce irinsa ake bukata a cikin al’umma.

Leave a Reply