Uncategorized

Gwamnti mai ci ta Jefa yan’ Bauchi cikin
Talauci, inji Sadiq Baba Abubakar.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Tsohon Shugaban Sojin saman Najeriya kuma dan takrar kujerar gwamna a karkashin jamiyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi, Sadique Baba Abubakar yace gwamnatin jihar tayi watsi da hidimar noma tun zuwanta karagar mulki a shekara 2019, inda yace hakan ya jefa dumbin manoma cikin rashin tabbas da kuma talauci.

Sadique Baba Abubakar wanda bayyana hakanne yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a karaman hukumar Misau, yayi alkawarin farfado da tattalin arzikin jihar ta fannin noma a dukkan fadin jihar in aka bashi dama a zaben 2023.

A lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsakin a dakin taro na Musamman, Abubakar ya nemi ganin cewa sun mara mashi baya a zaben dake tafe a watan uku cikin wan shekarar.

“yace gwamnatin jiha ta gagara lalubo mafita ta hanyar cire miliyoyin alummar jihar Bauchi cikin kangin yunwa da halin kaka ni kayi da rashin aikin yi ga matasa da mata.

Ya kara da cewa, yau a jihar Bauchi talaka baya iya cin abinci sau uku a gidansa, a cewarsa talauci yana kara ta’azzara a fadin jihar.

“Don haka gwamntinmu zata tashi tsaye ta gyra wan nan matsala”, inji Ambasada Sadique.

Tun a farko dan takarar ya zauna da yan’ kasuwa a karamar hukumar inda yayi masu alkawarin samar da hanyoyin raya kasuwanchinsu.

Tsohon sojan yana ci gaba da jan hankalin alumman jihar a lokacin gangamin kampe, da su yadda da manufofinsa su zabe shi a matsayin gwamnan jihar don chanji mai dorewa da walwala a cikin rayuwar talaka.

Leave a Reply