Uncategorized

2023: Atiku Na Kan Gaba A Kananan Hukumomi 6 Na Jihar Bauchi

Daga Khalid Idris Doya

A cigaban da amsar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 daga kananan hukumomin jihar Bauchi, zuwa yanzu Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP shi ke kan gaba da rinjaye mai gwabi kan sauran abokan hamayyarsa.

Sakamakon da aka bayyana Kai tsaye daga Cibiyar tattara sakamakon da ke Shalkwatar INEC a Bauchi, ya yi nuni da cewa a karamar hukumar WARJI APC ta samu kuri’u 11,862; PDP 17,732; NNPP 424 da kuma LP mai kuri’u 185.

Karamar hukumar Bogoro kuwa APC 4,850; LP 6,866; NNPP 798 sai kuma PDP 15,156.

Karamar hukumar Dass, APC 10,939; LP 705; NNPP 397; sai kuma PDP mai kuri’u 13,242.

A karamar hukumar Jama’are APC 8,410; LP 22; NNPP 3,638; PDP12,535.

Dambam, APC 7,588 LP 42; NNPP 2,586; PDP 12,203.

GIADE, PDP 11,977; APC 10,382; NNPP 4002; LP 17.

Karamar hukumar Darazo APC 16,070; PDP 17,459; NNPP 1,895.

Kananan Hukumomin 7 aka yi a cikin 20 zuwa yanzu. Kawo yanzu PDP ke rinjaye a jihar Bauchi yayin da ake zaman jiran sauran kananan hukumomi zuwa yanzu haka karfe 6:18pm.

Leave a Reply