Tinubu Ya Rattaba Hannu A Dokar Ba Da Rance Ga Dalibai
Daga Khalid Idris Doya
A wani mataki na cika alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe na kyautata sashin ilimi, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu kan dokar lamunin rance ga dalibai.
Dokar za ta taimaka ne kai tsaye ga dalibai da kudi ke zama musu cikas wajen cigaba ko yin karatu a manyan makarantun gaba da sakandari.
Mambar kwamitin yada labarai na kwamitin yakin zaben shugaban kasa, Mista Dele Alake, shi ne ya shaida hakan a hirarsa da ‘yan jarida da yammacin ranar Litinin.
Ya ce, kudaden rancen za su kasance a karkashin kulawar ma’aikatar ilimi kuma dalibai ‘yan asalin kasa wadanda ba su da karfi da suke manyan makarantu ne kawai za su iya samu cin gajiyar wannan sabon tsarin.
Alake ya ce, dokar an samar da ita ne domin taimaka wa daliban Nijeriya su samu ilimi a kasar nan ba tare da Shan wahala ko tsaiko ba.
“Ina farin cikin sanar da ku cewa a yau, mintina kadan da suka gabata, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan dokar bai wa dalibai rance.”
“Wannan na daya daga cikin alkawuran da Bola Ahmed Tinubu ya yi kamfen da su.”
Kudurin dokar lamunin rancen wacce Kakakin Majalisar Dokokin tarayya ta 9, Femi Gbajabiamila, ya gabatar, ta samar da tanade-tanaden samar da bashi da babu ruwa a ciki domin dalibai ‘yan asalin Nijeriya da basu da karfin tattalin arziki su samu damar yin karatu a saukake, tunin mako biyu da suka gabata kudin ya tsallake karatu na uku.
Dokar ta kawo wani sabon tsari ta yadda dalibai za su samu zarafin karbar rance marar ruwa ta asusun rancen ilimi ta Nijeriya ‘Nigerian Education Loan Fund.’