Gwamnan Jihar Gombe Ya Kafa Majalisar Ba Da Shawarori
Daga Khalid Idris Doya
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya kafa majalisar ba shi shawarwari don taimakawa wajen tsarawa da aiwatar da manufofi da tsare-tsaren tafiyar da Jihar.
A cewar gwamnatin jihar, an kafa majalisar ce da nufin bunkasa tattalin arziki, da yaki da talauci, da rashin aikin yi da sauran kalubalen tattalin arziki da zamantakewa da jihar ke fuskanta.
Wata sanarwa da Babban Daraktan Yada Labarai da hulda da manema Labarai na gidan Gwamnatin jihar, Ismaila Uba Misilli ya fitar, ta bayyana ce, Majalisar na karkashin jagorancin Farfesa Idris Mohammed ne, kwararre a fannin ilimi da kiwon lafiya wanda ke da kwarewa ta tsawon shekaru da dama a Nijeriya da kasashen ketare.
“Bugu da kari, Farfesa Mohammed ya shahara wajen yin amfani da dimbin damammakin da Jihar Gombe ke da su, musamman a fannin kiwon lafiya da ilimi,” in ji Misilli.
Ya ce mambobin majalisar bada shawarar wadanda aka gwada aka tabbatar da gaskiya da nagartarsu, kuma suka kai kololuwar ayyukan su, “Ana sa ran za su yi amfani da kwarewarsu ta kowane fanni wajen gudanar da ayyukan da suka dace don karfafa nasarorin da aka cimma a fannin shugabanci na gari a Jihar Gombe don samar mata kyakkywar makoma.”
Sanarwar ta zayyano mambobin kwamitin kamar haka, Dr Ibrahim Jalo Daudu (Mamba): tsohon Babban sakatare mai ritaya a Gwamnatin tarayya, kuma tsohon shugaban ma’aikatan gwamnati; Dakta Daudu kwararre ne a fannin yi wa gwamnati garambawul da inganta ayyukan ci gaba mai dorewa.
Sauran su ne: “Malam MK Ahmad (Mamba): Malam Ahmad kwararren ma’aikaci ne kuma gogagge a fannin bunkasa tattalin arziƙi, da hada-hadar kudi; Micah I Jimeta (Mamba): kwararren ma’aikaci ne a fannin jagorancin jama’a tare da kwakkwarar shaida ta jagorancin al’umma; Farfesa Fatima B.J. Sawa (Mamba): Farfesa Sawa, Tsohuwar Shugabar Kwalejin Aikin Gona ta Tarayya dake Dadinkowa, kwararriyar masaniya ce a fannin muhalli da bunkasa aikin gona wacce ta taka rawa wajen tsara manufofin kare muhalli da habaka aikin gona.
Sauran sun hada da, Injiniya Sa’idu Aliyu Mohammed (Mamba): jigo ne a harkar mai da iskar gas; Arch Suleiman Mohammed Kumo (Mamba): Baya ga kasancewarsa tsohon daraktan Babban Bankin Nijeriya, yana da masaniyar aiki a fannin samar da kudade da ci gaba; Prof. Baba Yusuf Abubakar (Mamba), babban shehin malami ne a fannin kimiyyar dabbobi wanda ya kasance kan gaba wajen bincike da tsara manufofin bunkasa noma a Nijeriya da ma duniya baki daya.
Sauran su ne, Injiniya Abubakar Bappah (Mamba), wanda tsohon kwamishinan Ayyuka da Sufuri ne na Jihar Gombe, ya tsunduma cikin samar da muhimman ababen more rayuwa a Jihar tun a shekarar 1996; Dakta Muazu U. Shehu (Sakatare): shine Babban Daraktan Sashin Bincike da Adana Bayanai na Jihar Gombe.