DARUSAN RAMADHAN
Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia
Darasi na biyu: Falalan Azumi
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi aiyukan Ibada don ya tsarkake su, ya daukaka su a wajensa, su samu yardarsa da sakamako mai girma.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, da iyalan gidansa, da Sahabbansa.
Ya ku ‘yan’uwana, ku sani Azumi yana cikin aiyukan Ibada mafiya falala, yana cikin manyan aiyuka da’a ma Allah, an ruwaito Hadisai masu yawa a kan falalolinsa.
Daga cikin falalolinsa Allah ya wajbata Azumi a kan dukkan al’umomi, ya farlanta shi a kansu. Allah ya ce:
{Ya ku wadanda suka yi Imani, an wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku, don ku samu tsoron Allah} [al-Baqara: 183].
Kasancewar Azumi Ibada ce mai girma, wacce Allah yake sonta, kuma dukkan bayi ba za su wadatu da barinta ba, da abin da za a samu a kansa na lada mai girma shi ya sa Allah ya wajabta shi a kan dukkan al’umomi.
Daga cikin falalolin Azumi sababi ne na gafarta zunubai da kankare kurakurai, ya tabbata Annabi (saw) ya ce:
((Duk wanda ya azumci watan Ramadhan, yana mai Imani da neman lada to za a gafarta masa zunubansa da suka gabata)). Sahihul Bukhari (38), Sahihu Muslim (760).
Abin nufi; wanda zai samu gafaran shi ne wanda ya yi Azumin yana mai Imani da Allah, tare da yarda da farlancin Azumin a kansa, kuma a halin neman lada da sakamako a wajensa. Sabanin wanda ya yi Azumin a matsayin tilas a kansa, kuma yana mai shakkan samun lada a kan Azumin, to wannan kam Allah ba zai gafarta masa ba.
A wani Hadisin kuma, Annabi (saw) ya ce:
((Salloli biyar, da Sallar Juma’a zuwa wata Juma’ar, da Azumin Ramadhan zuwa wani Ramadhan din, masu kankare abin da ke tsakaninsu ne matukar an nisan manyan zunubai)). Sahihu Muslim (233)
Yana daga cikin falalolin Azumi ladansa ba a kayyade shi da adadi ayyananne ba, shi mai Azumi an aba shi ladansa ne ba tare da lissafi ba. Ya tabbata daga Annabi (saw) ya ce:
((Allah ya ce: dukkan aikin dan’adam nasa ne, sai dai Azumi, shi kam nawa ne, ni zan yi sakamako a kansa. Azumi garkuwa ne, don haka idan ranar Azumin dayanku ta zo, kar ya yi maganar batsa, kar ya yi hayaniya, idan wani ya zage shi ko ya neme shi da fada to ya ce: ni mai Azumi ne. Na rantse da wanda ran Muhammad yake hanunsa, warin bakin mai Azumi ya fi dadi fiye da kamshin turaren miski a wajen Allah. Mai Azumi yana da farin cikin guda biyu; idan ya yi bude baki zai yi farin ciki, idan ya hadu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da Azuminsa)). Sahihul Bukhari (1904), Sahihu Muslim (1151).
Wannan Hadisi mai girma yana nuni ga falalolin Azumi ta fiskoki masu yawa, daga ciki:
Fiska ta farko: Allah ya kebance Azumi a tsakanin sauran aiyukan Ibada ga kansa, saboda matsayinsa a wajensa, da sonsa da yake yi, da yadda Ikhlasin bayi yake bayyana ga Allah a cikinsa, saboda sirri ne tsakanin bawa da Ubangijinsa, babu mai sanin Ikhlasin bawa a cikin Azumi sai Allah. Saboda mai Azumi zai iya buya ya ci abinci, amma ba zai yi hakan ba, saboda ya san Allah yana ganinsa. Sai ya hakura don neman lada a wajen Allah. Shi ya sa Allah ya ce:
((Zai bar biyan sha’awarsa don ni)). Sahihul Bukhari (7492), Sahihu Muslim (1151).
Fiska ta biyu: Allah ya ce: ((Ni zan biya ladansa)). Sai ya jingina yin sakamako a kansa zuwa ga kansa, saboda aiyuka na kwarai ana ninka ladansu da adadi, kyakkyawan aiki daya za a ninka shi goma, har zuwa ninki dari bakwai, zuwa ninki masu yawa. Amma shi Azumi Allah ya jingina yin sakamako a kansa ga kansa ba tare da kayyade shi da wani adadi ba, Allah kuwa mai karamci ne, shi ya fi kowa karamci, kuma kyauta tana kasancewa ne gwargwadon matsayin mai yinta. Saboda haka lallai ladan mai Azumi zai kasance mai girman gaske, ba tare da lissafi ba.
Kuma shi Azumi, ya tattara dukkan nau’o’in hakuri; hakuri a kan da’a ma Allah, da hakuri a kan aiyukan da ya haramta, da hakuri a kan kaddaran Allah masu ciwo; na yunwa da kishirwa da raunin jiki, wannan shi ya tabbatar da kasancewar mai Azumi yana cikin masu hakuri, Allah ya ce:
{Kawai ana biyan masu hakuri ladansu ne ba tare da lissafi ba}. [al-Zumar: 10].
Fiska ta uku: Azumi garkuwa ne, ma’ana; makari ne da yake kare bawa daga yasasshiyar magana da basta, shi ya sa ya ce:
((Idan ranar Azumin dayanku ta zo, kar ya yi maganar batsa, kar ya yi hayaniya)). Kuma zai kare shi daga wuta, kamar yadda Annabi (saw) ya ce:
((Azumi garkuwa ne, bawa yana kare kansa da ita daga wuta)). Musnad Ahmad (14669).
Fiska ta hudu: Lallai warin bakin mai Azumi ya fi dadi fiye da kamshin turaren miski a wajen Allah, saboda warin bakin ya faru ne saboda Azumi, sai ya zama mai dadi a wajen Allah kuma abin so gare shi. Wannan dalili ne a kan girman lamarin Azumi a wajen Allah, ta yadda har abun ki, abun kyama a wajen mutane zai zama mai dadi abin so a wajen Allah, saboda warin ya fito ne daga yi masa da’a ta hanyar Azumi.
Fiska ta biyar: Mai Azumi yana da farin cikin guda biyu; farin ciki a lokacin bude baki, da farin ciki a lokacin haduwa da Ubangijinsa. Amma farin ciki a lokacin bude baki, zai yi farin ciki ne saboda Allah ya yi masa ni’imar aikata wannar Ibada ta Azumi, wacce tana cikin manyan aiyukan Ibada.
Amma farin cikinsa a lokacin haduwa da Ubangijinsa, zai yi farin ciki ne saboda zai samu sakamakonsa cikakke a wajen Allah, a lokacin da ya fi bukatarsa, a lokacin da za a ce:
((Ina masu Azumi? Ku zo ku shiga Aljanna ta kofar RAYYAN, idan na karshensu ya shiga sai a rufe kofar)). Musnad Ahmad (22818), Sahihul Bukhari (1896), Sahihu Muslim (1152).
Kuma a cikin wannan Hadisi akwai koyar da mai Azumi abin da zai yi idan wani ya zage shi ko ya nemi shi da fada, kar ya biye shi, kuma kar ya yi masa shiru, a’a, ya ce masa: Ni mai Azumi ne, don ya nuna masa cewa; girmama Azumi ne ya sa ba zai biye shi ba, ba don gazawa ba.
Daga cikin falalolin Azumi zai ceci mai yinsa a Ranar Qiyama. Ya tabbata Annabi (saw) ya ce:
((Azumi da Alkur’ani za su ceci bawa a Ranar Qiyama, Azumi zai ce: Ya Ubangiji, na hana shi abinci da biyan sha’awarsa da rana, ka ba ni cetonsa. Alkur’ani ma zai ce: na hana shi bacci da daddare, ka ba ni cetonsa, ya ce: Sai su yi ceto)). Musnad Ahmad (6626).
‘Yan’uwa, ba a samun falalolin Azumi sai mai Azumi ya lazimci laduban Azumin, don haka ku yi kokari wajen kyautata Azuminku, da kiyaye shi, ku tuba ga Ubangijinku, ku nemi gafarsa.
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu.