Hausa

Fadi Tashin Gwamna Inuwa Yahaya A Abuja

Rubutawar Ismaila Uba Misilli

A kwanakin bayan nan ne Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya shafe wani lokaci a Abuja, don ci gaba da kokarin sa na bunkasa tattalin arzikin jihar, da jawo hankalin masu zuba jari, da inganta walwalar al’ummar jihar dama bunkasa jihar.

Gwamna Inuwa Yahaya ba ya cikin gwamnonin dake rawar kafa kan lamarin Abuja, amma yana ziyartar babban birnin kasar ne lokacin da ya zama tilas bisa manufa mai ma’ana don ciyar da jihar gaba. Idan aka yi la’akari da abubuwan da suka samo asali daga irin wannan ziyarar tasa, a bayyane yake cewa abubuwa da aka cimma na baya-bayan nan zasu haifar wa jihar ɗa mai ido.

Kwanannan ne Abuja Gwamna Inuwa ya ziyarci manyan ministoci biyu da suka hada da; ministan ayyuka Babatunde Fashola da takwaransa na Ma’aikatar makamashi, Engr Abubakar Aliyu. Ya kuma gana da Shugaban hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta Kasa, NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Jihar Gombe.

Gwamnan na jama’a, a yayin daya ziyarci Ma’aikatar Ayyuka ya koka kan lalacewar wasu hanyoyin gwamnatin tarayya a Gombe da sauran jihohi biyar makwabta, musamman hanyoyin Bauchi zuwa Gombe, da Gombe zuwa Kwami zuwa Dukku zuwa Darazo, da kuma Gombe zuwa Biu, da Gombe zuwa Potiskum da hanyar Gombe zuwa Numan zuwa Yola.

Wannar bukata ta gwamnan na zuwa ne bayan da ya gina hanyoyi kusan kilomita 340 a fadin kananan hukumomi 11 na jihar a karkashin shirin sa na network 11-100, shirin gina hanyoyin kilomita 100 a kowace karamar hukuma.

Don haka, bukatar da yayi na gaggauta gyara tabarbarewar hanyoyin tarayya wani yunkuri ne na jin ƙan ɗan adam da Gwamnan ke dashi wanda ke ci masa tuwo a kwarya.

Kalaman Gwamna Inuwa Yahaya sun bayyana gaskiyar sa yayin da ya ce “Na zo ganin mai girma Minista ne musamman game da halin da wassu manyan hanyoyin tarayya ke ciki. Kun sani cewa Gombe tana tsakiyar Arewa maso Gabas. Duk sauran jihohi 5 na Arewa maso Gabas. suna da iyaka da Gombe, ma’ana muna da hanyoyin mota waɗanda mallakar tarayya ce tsakanin Gombe da sauran jihohin, galibin waɗancan hanyoyin suna fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a wannan shekarar, kuma suna buƙatar kulawa ta gaggawa.”

“Na kuma zo nan ne don jawo hankalin gwamnatin tarayya don gyara wadannan hanyoyi, idan ba haka ba kuwa, alaka zata yanke tsakanin Jihar Gombe da sauran jihohi wadda kuma hakan zai yi muni”.

A Ma’aikatar makamashi kuwa, gwamnan ya bukaci Ministan Engr Abubakar Aliyu da ya dau matakan gaggawa don ganin an amfana da madatsar ruwa ta Dadinkowa don amfanin mutanen Gombe da bunkasa tattalin arzikin yankin.

Gwamnan ya ce samar da wutar lantarki shine mabuɗin ci gaban walwala da tattalin arziƙi, ya kara da cewa tabbatar da aikin madatsar zai tabbatar da zuba hannun jari na Gwamnatin Tarayya.

Bugu da ƙari, gwamnan mai tunani, dabaru da hangen nesa, ya fahimci mummunan tasirin ta’ammuli da miyagun kwayoyi akan tsaro da jin daɗin jama’a, hakan tasa ya tuntubi Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) don neman ƙarin haɗin gwiwa.

Gwamnan ya bayyana cewa akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin amfani da miyagun ƙwayoyi da aikata laifuka a cikin kowace al’ummah.

Yace daya daga cikin abubuwan dake kara rura wutar aikata miyagun laifuka, musamman tashin hankalin dake faruwa a Arewa maso Gabas, ana iya danganta shi da amfani da ta’ammuli da haramtattun kwayoyi wanda galibi ke gurbata hankali da tunanin dan adam.

“Cikin shekaru biyun da suka gabata, na samu fahimta sosai dangane da waɗannan batutuwan bayan dana zama Gwamna, a zahiri duk batutuwan suna ƙarewa ne a gaba na, kuma zamu iya magance kaso mai yawa game da batutuwan dake da alaka da miyagun kwayoyi “.

Ganawa ta baya-bayan nan da Gwamna Inuwa Yahaya yayi na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari inda ya gabatar da buƙatar bin diddigin yadda ake hako mai a Gombe tare da gabatar da shirin aikin Masana’antar dake gudana ga Shugaban a hukumance.

Babu shakka Gwamna Inuwa Yahaya ya jawo muhimman abubuwa ga Jihar Gombe ta hanyar hada hannu da yake yi da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, Jihar Gombe zata ci gaba da girbar gagarumin tasirin ziyarar da ya keyi, kamar yadda muke sa ran masu saka hannun jari sakamakon samun kambun jinjina na jihar da tafi saukin harkokin gudanar da kasuwanci.

Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe, ya aiko da ra’ayinsa daga Gombe

17 thoughts on “Fadi Tashin Gwamna Inuwa Yahaya A Abuja

Leave a Reply