News

Gwamnan Bauchi Ya Karya Farashin Taki Zuwa N20,000

Daga Khalid Idris Doya

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad a ranar Asabar ya ƙaddamar da fara sayar da takin zamani na daminar bana kan farashi mai rahusa da nufin bunƙasa harƙoƙin noma a jihar.

Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da daminar bana da fara sayar da takin zamani a farashi mai rahusa da ya gudana a ƙaramar hukumar Dass, gwamna Bala ya ce, gwamnatin jihar ta sanar da naira dubu 20 a matsayin kuɗin buhun takin zamani NPK guda.

Kazalika, gwamnan ya kuma ƙaddamar da sabbin Tiraktocin noma guda 60, sabbin Injunan noma domin ƙarfafa wa noman zamani, ƙari kan shirin tallafin kuɗi na dalar Amurka 250,000 ga zaɓaɓɓen ƙungiyoyin manoma a faɗin jihar.

Muhammad ya ce a bisa ƙoƙarin da suke yi kan shirye-shiryen da suka shafi noma, gwamnatinsa ta shirya samar da wasu ƙarin kayayyakin noma da ɗaukan malaman goma domin inganta samun amfanin gona.

Bala ya kuma nuna aniyarsa na ilmantar da manoma da dabaru da hanyoyin amfani da sabbin na’urorin noma na zamani. Ya kuma bada tabbacin cewa, za su yi duk mai yiyuwa wajen tabbatar da tsaro wa manoma domin ba su ƙwarin guiwar shiga gonakai domin noma ba tare da fargaba ko razani ba.

Ya nanata cewa gwamnatinsa ta ɗauki harƙar noma a matsayin abu mai muhimmanci lura da yadda yawancin ‘yan jiharsa suka kasance manoma.

Da ya ke jinjina wa gwamnatin tarayya da shirin inganta muhalli na bankin duniya wato ACReSAL da sauran abokan haɗaka, Muhammad ya sha alwashin ci-gaba da shiga lunguna da saƙo domin nemo tallafi ga manoman da suke jiharsa.

Kan ɗumamar yanayi, gwamnan ya ce, za su shuka ire-iren shukoki daban-daban bisa shawarorin kwararru domin kyautata tattalin arziki.

Kan hakan, gwamnan ya yi gargaɗin cewa, duk wani mutum ko gungun mutane da aka samu da sayar da takin gwamnati kan farashi fiye da wanda ya sanar, to lallai mutum zai ɗanɗana kuɗarsa.

Tun da farko, Kwamishinan Ma’aikatar gona na jihar Bauchi, Farfesa Simom Madugu Yelams, ya ce, ma’aikatarsa ta ɗauki dabarbarun da suka dace wajen ganin noma da suke sassan jihar lungu da saƙo sun samu zarafin sayen takin ba tare da shan wahalhalun ba.

Shi kuma shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Dass, Muhammad Jibo, ya yaba wa gwamnan Bala Muhammad kan shirye-shiryensa na bunƙasa harkokin noma a faɗin jihar.

Leave a Reply