Uncategorized

HAƊUWATA DA JARUMI SHU’AIBU LAWAN KUMURCI

Daga AMB Nazeeb Sulayman Ibraheem

Kamar shekaru 10 da suka wuce, wani fitaccen ɗan wasan kwaikwayo a Bauchi ya ziyarce ni a gidana shi da fitaccen ɗan wasan nan na Kano Kannywood, Shu’aibu Lawan (Kumurci). Wannan rana ita ce farkon saduwata da ‘Kumurci.’

Muna zaune a falona bayan mun kammala cin abincin rana, sai muka shiga taɗi. A harkar fim ni tsohon darekta ne. Babu ɗan jarida da zai samu digiri a harkar jarida sai ya taɓo ɓangaren wasan kwaikwayo. Akwai ƙungiyoyin wasan kwaikwayo da dama dana ƙirƙiro shekaru kamar 30 da suka wuce, wasu kuma 20 nan baya.

Jarumi Shu’aibu Lawan Kumurci yayi mamakin daɗewata a duniyar wasan kwaikwayo amma bai taɓa gani na ba sai a ranar. Danlami Yanke-Yanke wanda ɗalibina ne a harkar wasan kwaikwayo ya masa cikakken bayanin yadda aka faro harkar fim dani a Kano tare da Darekta Marigayi Tijjani Ibrahim, Bala Anas Babinlata, Ado Ahmad Gidan Dabino, Kwabon Masoyi, Ibrahim Mandawari, Tahir Fagge da sauran tsoffin ‘yan Kannywood. Tun bayan rasuwar babban Darekta Tijjani Ibrahim harkar wasan kwaikwayo ta fara cin karo da al’adun Malam Bahaushe. Kwabon Masoyi ya fita. Ni ma na fita jim kaɗan bayan fitaccen fim ɗin nan ‘Aisha Ki Yarda Dani.’

Kumurci lokacin bai shiga harkar ba. Ya shigo ne shekaru kusan 10 bayan mun ajiye hidimar. A lokacin zantawar tamu, Kumurci yana gumm yana jinmu. Wasu abubuwa da suka burgeni da Shu’aibu Lawan Kumurci sune sauƙin kai da fara’a. Babu wanda zai ga finafinan Kumurci yace zai yi sauƙin kai. To amma ai wasan kwaikwayo wasa ne.

Ko da muka zanta, muka baiwa juna lambar waya, muka fito zan raka su. Ashe labari ya game unguwata wai Kumurci na gidana. Yara maza da mata, manyan mata da mazaje an yi caa a ƙofar gidana ana jira Kumurci ya fito. Kai ranar na ga jama’a. Hanya ta toshe sai ihun “Kumurci…Kumurci…’ ka ke ji. Unguwa ta ɗauka. Shi kuwa gogan sai ya murtuke fuska irin ta Kumurci ya dawo ɗan daba nan take yana zare idanu yana ihu irin yadda yake yi a fim. Haba, yara kuwa suka ɗau ihu suna tsalle suna tafawa da jaruminsu; gwanin-ban sha’awa. Mun fi awa ɗaya muna fama da jama’a su yi haƙuri su kyale mu mu tafi, amma ina!

Can sai Kumurci ya ja zugar yara yana tafiya irin ta ‘yan daba yara na tsalle suna ihu irin na jaruminsu, suna bin sa ɗuu. Kumurci ya shiga wani shago ya saye biskit da mintin shagon tas ya raba wa yara. Sai ihu kake ji unguwa kamar zata tsage don ana ji da Shu’aibu Lawan Kumurci a ko’ina a ƙasar Hausa.

Bayan magiya da lallami muka shige mota muka wuce da ƙyar yara na bin motarmu da gudu suna kiran “Kumurci…Kumurci…!’

Bayan mun tsere daga matasan nan na ce:

” Amma Kumurci kana son yara.”

Yace,” Yallaɓoi kamar ka sani. Ai ni a nan duniya babu abinda ke sanya mun farin ciki kamar yara. Ko tun ina ɗan yaro ina son shiga safgar yara. Kowa ya sanni da haka a gida.”

Nace, “Na ga alama. Haƙiƙa Kumurci kana da farin jinin jama’a.”

Kun ji labarin farkon haɗuwata da gwarzon jarumi Shu’aibu Lawan Kumurci. Daga nan mun haɗu dashi kamar sau 3 ko sau 4 a Kano.

Tabbas, Shu’aibu Lawal Kumurci mutum ne mai natsuwa da kirki da son jama’a da tausayi. Zai yi wahala ka ga fushinsa a zahiri. Matsayinsa na fim dabam.

Godiya nike ɗan kirki. Allah Ya ƙara shiga lamurranka, Ya kare ka daga sharrin Shaiɗan, aljani da mutane. A gama lafiya. Godiya Danlami Yanke-Yanke ɗan amana. Allah shi ƙara basira da arziki. A gama lafiya.