Uncategorized

Hon. Bobbo Ya Yi Alkawarin Cigaba Da Taimaka Wa Addinin Islama

By Mohammed kaka Misau, Bauchi

Shugaban marasa rinyaje a Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Hon. Bakoji Aliyu Bobbo, ya sha alwashin cigaba da bada kokarinsa wajen taimaka wa Addinin Musulunci a kowani.

Dan Majalisar wanda ke wannan furucin a lokacin da ya karbi bakwancin kungiyar dalibai musulmai na kasa rashen jihar Bauchi da suka ziyarceshi a gidansa da ke Misau yau Lahadi.

Bobbo ya nuna godiyarsa bisa wannan ziyara tare da bada tabbacin dukkan abun da ya taso da ke bukatar gudumawarsa a duk bangarori na aiki zai yi iya bakin kokarinsa don ganin ya cigaba da bada nasa gudumawar kamar yadda ya saba.

Ya yaba wa kungiyar MSSN na Misau bisa kokari da himma da suke da shi wanda na daga cikin abubuwan da ke sa wannan kungiya take samun nasarori wajen gudanar da al’amuran ta, ya kuma kara da cewa kofa a bude take a dukkan lokacin ake bukatar gudumawarsa kan taimakawa addini zai yi iya kokarinsa.

A nasa jawabin shugaban MSSN na karamar hukumar Misau, Malam Hamza Nayola ya bayyana cewa, “Wadannan shugabanni daga matakin jiha sun kawo ziyara ne na musamman don yin godiya da zumunci ga shugabanni da ke taka muhimmiyar rawa gurin wurin taimakon wannan kungiya da addini musulunci baki daya.”

Hakazalika, cikin jawabinsa ya lissafa wasu muhimman ayyuka da taimakon addini da Hon. Bakoji ya ke yi wa wannan kungiya da kuma musulunci baki daya.

Mal. Hamza ya kara da cewa lallai Hon. Bakoji Bobba ya yi wa addini taimako da yawa inda yake kara da cewa ya gina masallatai da yawa da taimakawa marayu gurin aurensu da basu kulawa, da kuma kawo sabbin makarantu da dubai malaman wucin gadi da sauran abubuwan da ba za su misaltu ba.

A nashi jawabin shugaban MSSN na jihar Bauchi, Shiekh Rabi’u Baraubal ya yi godiya na musamman zuwa ga Minority leader bisa kokarin sa wajen taimakawa addini Allah dama kungiyar baki a daya.

Ya kuma kara da kiran ga Hon. Bakoji da ya cigaba da taimakawa wajen aikin Allah kaman yadda ya saba kar ya gajiya.

A nasu bangaren suma tawagar sun bayyana wani kuduri da kungiyar rashen jihar Bauchi ke bukata na samun wata doka da za ta daman cigaba a habaka Harker addini musulunci da wanzar da tarbiyyan addini da zamantakewa na yau da kullum daon samun sauki kan lamarin lalacewar tarbiya da ake ciki a halin yanzu.

Leave a Reply