Jami’ar MAAUN Ta Nemi Sabbin Ma’aikata Su Nuna Jajircewa Da Sadaukarwa A Ayyukansu
Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) da ke Kano, ta bukaci sabbin ma’aikatan da aka dauka wadanda ba karantarwa suke yi ba na jami’ar da su nuna sadaukarwa wajen gudanar da ayyukansu domin duk wanda aka samu da lalaci za a kore shi daga aiki.
Mataimakin shugaban riko a bangaren ilimi da tabbatar da inganci, Dakta Nura A. Yaro ne ya bayar da wannan umarni a lokacin da yake jawabi ga sabbin ma’aikatan da ba karantarwa suke yi ba a lokacin da ake gudanar da taron wayar da kan ma’aikatan a dakin taro na Makarantar Fasaha da kimiyyar Gudanarwa a jiya.
Ya ce aikin wayar da kan ya zama dole ne ta yadda za a bullo da ɗa’a da kuma ka’idojin da ake son kowanne ma’aikaci ya sani kuma ya kiyaye.
Ya ce akwai bukatar sabbin ma’aikatan da suka dauka aiki su rika ganin cewa sun yi sa’ar samun aiki a jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya domin ita ce jami’a mai zaman kanta mafi saurin bunkasa a kasar nan.
“A tarihin jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya babu wata jami’a mai zaman kanta da ta fara da mutane dubu sai MAAUN.”
Ya bayyana cewa akalla mutane 6,000 ne suka nemi gurbin samun aikin da ba na karantarwa ba a jami’ar, inda mutum 65 ne kawai aka yi nasarar tantance su tare da daukar su aikin.
Don haka ya bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu bisa dokoki da ka’idojin jami’ar domin duk wani aiki na rashin ɗa’a irin na rashin maida hankali da lalaci jami’ar ba za ta amince da su ba.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban MAAUN, Farfesa (Dr) Mohammad Israr ya taya sabbin ma’aikatan murnar aikin da suka samu, ya kuma bukace su da su ba da himma wajen gudanar da ayyukansu.
Shima a nasa jawabin, wanda ya kafa kuma shugaban Hukumar gudanarwa na Jami’ar MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya yi kira ga sabbin ma’aikatan da su kasance masu kwazo da gaskiya domin wannan shi ne mafarin nasararsu a jami’ar.
Farfesa Abubakar Gwarzo, wanda ya yi dogon bayani a kan tarihin jami’ar da aka fara kafawa a birnin Maradi na jamhuriyar Nijar, ya kuma shawarce su da su kasance masu zurfin tunani da bunkasa kansu ta hanyar zuwa karo karatu.
Ya ce jami’ar za ta tallafa wa duk wani ma’aikacin da ke son bunkasa kansa matukar sun nuna sadaukarwa da juriya wajen sauke nauyin da aka dora musu.
A yayin taron wayar da kan, shugabannin sashen tsaro da kuma Dakta Umar Lawal wanda shi ne mai kula da asibitin jami’ar suma sun bayar da takaitaccen bayani kan ayyukan da suke da su a sashen.