Uncategorized

JAWABIN GWAMNAN GOMBE GAME DA ZABEN SHUGABAN KASA DA KE TAFE

JAWABIN MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR GOMBE. MUHAMMADU INUWA YAHAYA (ƊAN MAJEN GOMBE), GAME DA ZABEN SHUGABAN KASA DAKE TAFE, WADDA YA GABATAR YAU JUMA’A 24/02/2023

Ya ku ƴan uwa na al’ummar Jihar Gombe,

  1. Duba da muhimmin nauyin dake kaina, ina farin cikin yi muku jawabi a yau game da zaɓe a tsarin mu na dimokuradiyya, da kuma buƙatar tabbatar da ganin zaɓukan sun kasance cikin lumana, ‘yanci, gaskiya da sahihanci.
  2. Nan da sa’o’i 24 ko ƙasa da haka, muna sa ran ku da sauran ‘yan Najeriya da suka cancanci zabe, zaku fita zuwa rumfunan zaɓen ku daban-daban don kaɗa kuri’un ku na zaɓen shugabannin da zasu tafiyar da al’amuran ƙasar nan na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.
  3. ‘Yancin zaɓar shugabannin mu yana daga cikin ginshiƙan al’adun dimokuradiyya. Yana inganta riƙon amana a harkokin mulki da kuma bada tabbacin miƙa mulki cikin kwanciyar hankali da lumana daga wata gwamnati zuwa wata. Ina ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da wannan tsari. Kimanin shekaru huɗu da suka gabata al’ummar Jihar Gombe suka zaɓe ni cikin ‘yanci don in zama gwamna. Haka nan kuma kun sake zaɓan Shugaba Buhari ya zama shugaban ku a karo na biyu.
  4. Don haka ni abin alfahari ne a gare in jagoranci Gombe a wannan muhimmin lokaci. Bani da wata manufa data wuce in ga kasar mu (musamman a Gombe) an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da adalci da gaskiya. Ina da ƙwarin gwiwa kan tsarin wannan zaɓe, da kuma ƙwarewar hukumomin tsaro. A cikin shekaru 4 da suka gabata, mun ga sabbin sauye-sauye da hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi da nufin inganta harkokin zabe. Ina godewa shugabannin INEC da Shugaba Buhari bisa jajircewa da kishin ƙasar su kan tabbatar da hakan.
  5. Ya ku ‘yan uwa al’ummar Jihar Gombe, gobe kuna da wata muhimmiyar dama da zaku yi amfani da ita wajen yanke hukunci, kan zaɓen sabon shugaban ƙasa wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya gama wa’adin mulkin sa na wa’adi na biyu, da kuma zaɓen wadanda zasu wakilce ku a majalisar dokokin ƙasa. Makomar ku tana hannun ku. Don haka ku yi amfani da ita cikin hikima ta hanyar zaɓar shugabannin da zasu taimaka wajen haɗa kan ƙasa, da inganta zaman lafiyarta da kuma samar da ci gaba ga ɗokacin ‘yan Nijeriya.
  6. Ina ƙira gare mu, mu tabbatar an gudanar da zaɓen nan cikin kwanciyar hankali da lumana. Ina ƙira ga jam’iyyun siyasa da ɗaiɗaikun jama’a da ƙungiyoyi, su guji tashin hankali da tunzura jama’a kafin da lokacin dama bayan zaɓen. Hukumomin tsaro a shirye suke su tabbatar cewa masu kaɗa kuri’a sun samu damar yin hakan ba tare da wani tsoro, fargaba ko tsangwama ba; kuma zasu yi maganin duk wani ɗan siyasa ko ƙungiya dake neman tada fitina.
  7. Zaman lafiya da haɗin kai da kwanciyar hankalin Jihar Gombe (dama Najeriya) ya fi siyasar ko wane mutum ko ƙungiya. A matsayina na gwamna kuma babban jami’in tsaron Jihar Gombe, na yi rantsuwar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da muke dashi. Ba zan lamunci duk wani yunƙuri na kawo cikas ga zaɓukan da za a yi ba don neman biyan wata mummunar buƙata ko manufar wani mutum ko ƙungiya.
  8. Mu a Jihar Gombe, muna da al’adar zaman lafiya duk da bambance-bambancen da muke dashi amma muke mutunta juna akan su sosai. Tun a jamhuriya ta ɗaya, Gombe ta yi shura da zaman lafiya da rashin tashe-tashen hankula na siyasa,. Muna shiga zaɓe a matsayin iyali guda, ba tare da zagi, gaba, ko ƙyama ba. Na himmatu wajen tabbatar da wannar al’ada, da kuma bada dama ga jama’ar mu don su kaɗa ƙuri’ar su cikin ƴanci da walwala.
  9. Annobar labarun ƙarya, da kalaman ƙiyayya da yaƙin neman zaɓe na tunzura jama’a suna ci gaba da yin barazana ga gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali a faɗin duniya. Duba da bunƙasar kafofin sada zumunta na zamani, yana da wuya a iya kula ko daƙile hakan. Yaƙi da wannan ƙalubale alhakin mu ne duka. Ina ƙira ga masu ruwa da tsaki su daina ƙirƙira da yaɗa labaran ƙarya da farfagandar siyasa, ko kuma shiga duk wata dabi’a da zata kawo cikas ga ingantaccen zaɓe.
  10. Shugabannin mu na addini dana gargajiya suna da rawar da zasu taka wajen ganin an gudanar da zaɓen 2023 cikin tsari. Ina gode musu bisa haɗin kai da kishin ƙasa da suke bayarwa ya zuwa yanzu. Ina ƙira gare su, su ƙara zage damtse da addu’o’in ganin an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma su guji duk wani yunƙuri na tada ƙayar baya da tashin hankali. Ina kuma ƙira ga sarakunan mu su ci gaba da zama iyaye kamar yadda suka saba, kuma su ƙara sadaukarwa kan talakawan su.
  11. Ina yabawa jami’an tsaron mu bisa jajircewar su da kuma biyayyar su ga ƙasa. Hukumomin tsaro suna bada muhimmiyar kariya ga demokraɗiyyar mu. Ta hanyar sadaukarwa da jajircewar ku, kuna aiki ba dare ba rana don kare demokraɗiyyar mu daga maƙiya na ciki da waje. Ina tabbatar muku da goyon baya da haɗin kai na a ko da yaushe.
  12. Ga ƙungiyoyin fararen fula da suka haɗa da tawagar masu sanya ido kan zaɓe na cikin gida dana ƙasashen waje, ina ƙira a gare ku, ku yi aikin ku da kishin ƙasa da tsoron Allah. Ku tuna cewa zaɓe zai wuce, amma Najeriya zata ci gaba da wanzuwa. Dole ne ku doge kan aikin ku, ku guji barin wassu ƙungiyoyi na cikin gida ko na waje su yi amfani da ku don neman ɓata sunan kasar mu.
  13. A ƙarshe ina ƙira ga jama’ar mu su ci gaba da bin tafarkin zaman lafiya da haƙuri da juna. Bai kamata banbancin ra’ayin siyasar mu ya shafi alaƙar mu da, abokai ko maƙwabta ba. Mu yi zaɓe cikin kwanciyar hankali, mu yi musabaha mu rungumi juna, mu jira sakamakon zaɓe. Duk yadda sakamakon ya kasance, mu miƙa al’amuran mu ga Allah Ta’ala, domin shine mafificin wadda ke jiɓintan lamarin. Shi yake bada mulki ga wanda ya so a lokacin daya so.
  14. Da wadannan ‘yan jawabai nake yi mana fatan alheri, da yin zaɓuka na gaskiya, da adalci. Na gode da sauraro na da kuka yi. Allah ya muku albarka!

Allah Ya Albarkaci Jihar Gombe!
Allah Ya Albarkaci Tarayyar Najeriya!!

Leave a Reply