Yadda Matashi Ke Farfasa Kabura Don Zaro Roduna Don Samun Kuɗin Sayen Abinci A Bauchi
Daga Khalid Idris Doya
Wani Matashi mai suna Dauda Sa’idu mazaunin unguwar Yelwa, ɗan shekara 21 a duniya, ya faɗa tarkon ‘yansanda a jihar Bauchi bisa zarginsa da bin dare ya na farfasa Kaburburan da aka bisne matattu domin samun ƙarfen rodi.
Daga cikin dalilin wanda ake zargin na yin hakan shi ne domin samun damar sayar da rodunan domin samun kuɗaɗen sayen abinci da tabar wiwi.
‘Yansanda dai su na zargi matashin da kutse cikin maƙabarta, ɓarnata kabura da kuma laifin sata.
‘Yansanda sun ce, wanda aka tsaren ya kasance na bin tsakiyar dare wajen shiga cikin maƙabartar Kiristoci da ke Yelwan Kagadama a cikin garin Bauchi ta ɓarauniyar hanya, inda ya janyo lalata kabura da daman gaske da kuma cire rodunan da aka yi amfani da su wajen biso.
A wata sanarwar manema labarai da Sufuritandan ɗansanda, Ahmed Muhammed Wakil, jami’in watsa labarai na rundunar a jihar Bauchi ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, bayan tuhumar da suka yi da tambayoyi ga Sa’idu, ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa.
Shi dai Sa’idu ya ce, ya cire rodunan da dama inda yake sayar da su kama daga N9,500, N12,000, har 5,500, bi-da-bi.
Saidu ya kuma faɗa cewa yana amfani da kuɗaɗen wajen sayen tabar wiwi da kayan abinci domin amfanuwarsa.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya umarci a gurfanar da Sa’idu a gaban ƙuliya mance sabo da zarar aka kammala gudanar da bincike.
Kwamishinan ya bayyana muhimmancin da ake akwai na iyaye suke sanya lura kan motsin ‘ya’yansu a kowani lokaci.
l