Hausa

‘Yansanda Sun Musguna Min Don Mun Fito Neman Hakkinmu – Shugaban Nakasassu

  • Ba Zan Lamunci Duk Wata Nau’in Tauye Hakkin Bil-adama Ba – Gwamnan Bauchi

Daga Khalid Idris Doya

An shiga nuna takaici sakamakon yaduwar wani hoto mai motsi da ke nuna yadda wasu ‘yansanda suka musguna ma wani mai fama da bukata ta musamman Hamza Waziri a kofar gidan gwamnatin jihar Bauchi yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a ranar Alhamis.

Wakilinmu ya labarto cewa shi dai Waziri ya jagoranci wasu masu fama da bukata ta musamman domin shiga ayarin masu zanga-zangar neman kawo karshen shugabanci marar kyau da neman a dawo da tallafin mai a jihar Bauchi.

A bidiyon da wakilinmu ya gani, an ga yadda wasu ‘yansanda da kakinsu sun yi ruf wa Hamza Waziri a yayin da ke kan keken guragu a kokarinsu na korarsu daga kofar gidan gwamnatin.

A hirarsa da wakilinmu, Hamza Waziri wanda shi ne shugaban kungiyar ‘Initiative for the liberalisation of physically challenged people in Nigeria’ ya nuna takaicinsa kan yadda aka zalumce shi da yi masa dukan tsiya.

Ya ce: “Mun gudanar da zanga-zangar lumana abun takaici an musguna min an keta min hakki. Wannan abun takaici ne matuka. Meye laifina, kawai don muna zanga-zangar lumana sai a musguna min a kofar gidan gwamnatin Bauchi, wacce irin demukuradiyya muke?.”

“Na fuskaci musgunawar ‘yansanda ne a kofar gidan gwamnatin jihar Bauchi yayin da muke bayyana hakkinmu da doka ya ba mu. Daya daga cikin ‘yansandan sunansa AS Shira.

“Abun kaito shi ne an kafa ‘yansanda domin kare rayuka da dukiyar al’umma, amma lamarin ya juya ya zama mugunawa. Meye laifina ko don ni mai fama da bukata ta musamman ne?

“Ba mu da ayyukan yi, ba a ba mu damarmaki, da wariyar da ake nuna mana su na daga cikin dalilan da suka sanya na shiga zanga-zangar ni da sauran takwarorina, a maimakon a saurari kokenmu sai ya juya da musguna min.”

Hamza Waziri ya nuna bakin cikinsa da takaici, inda ya yi kira ga hukumomi da su tabbatar da kwato masa hakkinsa domin a cewarsa, “Ni ban ga laifin da muka yi ba, zanga-zangar lumana muka fito bisa dogara da sashi na 40 na kundin tsarin mulkin kasa.”

Ya koka da ,”A Bauchi kam bamu dau kayan kowa ba; amma mun sha duka.”

Sai dai nan take bayan faruwar lamarin, gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya fito ya yi tir da zargin da ake wa ‘yansandan na musguna wa mai fama da nakasan.

Bala ya ce, koda wasa gwammatinsa ba za ta lamunci kowani irin tauye hakkin jama’a ba.

A wata sanawar manema labarai daga fadar gwamnatin jihar ta nuna takaici da damuwa kan lamarin da ya faru tsakanin mai fama da bukata ta musamman da jami’an tsaron.

Sanarwar mai dauke sanya hannun kakakin gwamnan, Mukhar M. Gidado na cewa, “Muna son mu bayyana balo-balo ce wa Gwamnatin jihar Bauchi a karkashin jagorancin gwamna Bala Mohammed ba za ta lamunci kowani irin tashin tashin hankali ko rashin da’a daga kowani jami’in tsaron da ke aiki a gidan gwamnati ko wani jami’in gwamnati ba.”

Sanarwar ta ce tabbatar da jin dadi da walwar jama’a da kare musu hakki shi ne gwamnan Bala ya sanya a gabansa.

Don haka ne Mukhar Gidado ya sanar da ce wa, gwamnati za ta kaddamar da bincike kan abun da ya faru domin gano hakikanin abun da suke akwai kan wannan zargin.

Ya tabbatar da cewa dukkanin jami’in da aka samu da laifi tabbas za a hukunta shi daidai yadda ya dace.

Mukhtar Gidado ya nemi al’umma da su cigaba da kasance masu biyayya wa doka da oda a kowani lokaci musamman a irin wannan lokacin da ake zanga-zangar gama gari a fadin kasar.

Leave a Reply