Hausa

Ɗan Sanda Ya Hallaka Mahaifinsa Tsohon ASP A Maiduguri

 

Daga Khalid Idris Doya 

Jami’in ɗansanda mai muƙamin Sajent, Sunday Wadzani, ya kashe mahaifinsa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno biyo bayan ɓarkewar husuma da rashin fahimta a tsakaninsu. 

Rahotonni sun ce, Sunday ya buɗe wuta kan mahaifinsa har sai bakwai, inda ya bindige shi har lahira. 

Daily Trust ta tattato cewa lamarin ya faru ne a bayan shalkwatar rundunar ‘yansandan jihar da ke Modugannari, a ranar Lahadi.

Wanda ake zargi da wannan ɗanyen aikin, na aikin hidimar tsaro ne a majalisar dokokin jihar Borno. 

A cewar majiyar tsaro, tunin aka cafke Wadzani da tsare shi a caji ofis ɗin ‘yasanda da ke GRA. 

“Ɗan sanda mai suna Sgt. Sunday Wadzani da ke aiki a ƙarƙashin shalkwatar rundunar ‘yansandan jihar Borno a ranar 21 ga watan July 2024 ya bindige mahaifinsa har sai bakwai biyo bayan wata ‘yar ƙaramar husuma da ta shiga tsakaninsu,” cewar bayanin faruwar lamarin. 

Duk ƙoƙarin jin ta bakin jami’in watsa labarai na rundunar ‘yansandan jihar ASP Kenneth Daso, Kan wannan lamarin ya citura. 

Leave a Reply