Hausa

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Inuwa Yahaya A Matsayin Gwamnan Gombe

Kotun Koli ta tabbatar da zabin Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin halastaccen Gwamnan jihar Gombe.

Wannan matakin na zuwa ne bayan da kotun ta kori karar da jam’iyyar PDP da dan takararta Jibrin Barde suka shigar bisa cewa karar bai da inganci.

Kotun mai alkalai biyar a karkashin gagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta jaddada hukuncin da kotun daukaka Kara ta yanke na tabbatar da Inuwa a matsayin Gwamnan.

Wannan matakin ya kai ga tabbatar da Inuwa a matsayin Gwamnan jihar Gombe karo na biyu a karkashin jam’iyyar APC.

Leave a Reply