Zaben Cike Gurbi: PDP Ta Tafka Magudin Sayen Kuri’u – Sanatan Bauchi Ta Kudu, Buba
Daga Khalid Idris Doya
Sanatan Bauchi ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Shehu Buba Umar ya yi zargin cewa Gwamnati mai ci a jihar Bauchi (PDP) ta tafka mugudi na sayen kuri’u a wajen masu jefa kuri’a a yayin zaben cike gurbi kujerun ‘yan majalisan dokokin jihar Bauchi su hudu.
Sanatan wanda ya shaida hakan a lokacin da keu ganawa da ‘yan jarida dangane da yadda zaben ke gudana a jihar Bauchi ranar Asabar.
Ya ce tunin suka sanar da hukumomin tsaro korafin da suke da shi na sayen kuri’u da kuma kame musu magoya baya da aka yi a yayin gudanar da zaben.
Buba ya jinjina wa hukumar zabe bisa yadda ta yi tsare-tsare masu kyau, sannan ya ce hukumomin tsaro su ma sun yi tsare-tsaren daU suka dace na tabbatar da tsaro a yayin zaben.
Ya ce: “Daga rahotonnin da muke samu zaben na tafiya, sai dai ‘yan abubuwan da ba za a rasa ba na koke-koke, shi ne muke ta karban rahotonni daga mazabu.
“Yawancin koke-koken da muka samu yawanci, ka san mu a jam’iyyar APC mu a nan jam’iyyar adawa muke, kuma muna fuskantar Gwamnati mai ci.
“Muna da labarin Gwamnati ta fito da kudi su na sayen kuri’a, kuma sun tura manya-manyan mutanensu an je ana tsorata mutanenmu ana sayen kuri’a.”
Ya kara da cewa akwai korafin da suka da shi na cewa an kama musu ‘yan jam’iyyar APC a yankin Liman Katagum.
Dan majalisar ya nemi jama’a da su zaben bisa kwanciyar hankali ba tare da wani tashi hankali ba. Inda ya nuna gamsuwarsa kan yadda jama’a suka yi dafifi wajen fitowa a dama da su.
Ana sake gudanar da zaben ne a kujerun ‘yan majalisun dokokin jihar Bauchi su hudu.
A zantawarsa da ‘yan jarida kan wannan zargin, Kakakin jam’iyyar PDP Alhaji Yayanuwa Zainabari ya ce babu wani gaskiya a wannan zargin.
Ya ce babu wasu jami’ai da suka tura rumfuna domin razana masu zabe, “Akwai jami’an tsaro a ko’ina kuma sun gudanar da aikinsu yadda ya dace.
“Kawai ba su da kwarin guiwa ne shi ya sa suke wannan zargin,” Ya shaida .