Hausa

Ranar Shari’ah : Gomna Bala ga Alkalai, Ku hanzarta yanke hukunci ga wadanda suka aikata laifuffuka.

By: Sani Adamu Hassan.

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed.

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya kirayi Alkalai dasu kasance masu zaman kansu su kuma rika tsayuwan daka wajen yanke hukunci batare da nuna wata banbanci ba.

Gwamnan yayi wannan jawabinne a wajen taron ranar shari’ah na shekarar 2020,bisa cewarshi matukar anaso fannin shari’ah yayi tsayuwar daka tou akwai bukatar dogewa wajen yaki da dukkanin katsalanda daga waje.

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bukaci da a dinga hanzarta yanke hukunci ga wadanda ake zargi da aikata laifuka, don rage cunkoson a gidajen gyaran tarbiyya da kuma rage ayyukan ta’addanci a fadin jihar Bauchi.

Gwamnan wadda ya ke ba da fifiko wa tabbatar da adalci da gaskiya hadi bin doka da oda da kuma tabbatar da cin gashin kai cikakken wa sashin shari’ah don aiwatar da aikin su yadda ya kamata.

A karkashin ayyukan wannan shekarar, gwamnatin ta kammala ginin sashi na biyu na kotuna 8, zauren zaman alkalai, wajen yin rajistar shari’ah, wuraren ajiye mutane a kotu da dai sauran su.

Har wa yau anyi aikin gina sashi na biyu na babban kotu, da kuma kwaskwarima wa kotun da ke Fadamar Mada da kuma kammala aikin tsohuwar babbar kotu ta takwas izuwa guda biyu daban-daban.

Sauran ayyukan sun hada da sayo sabbin motocin aiki wa manyan alkalai, Manyan Khadi, Alkalan manyan kotuna da kuma dukkanin Khadin kotun daukaka kara.

Dangane da walwalar ma’aikatan shari’ah kuwa, gwamnan yace ya biya alawus-alawus din lafiyar alkalai da kuma kudaden gudanarwar bangaren shari’ah na wata-wata.

Tun farko da take jawabi Alkalin Alkalan jihar Bauchi mai shari’ah Rabi Talatu Umar tace ranar shari’ah ta wannan shekara ta bibiyi shari’un da aka gudanar a wannan shekarar da muke ciki domin tabbatar da ingantuwar shari’ah sannan ta tabbatar da nuna gwanancewan alkalai wajen tabbatar da shari’u.

Sai kuma ta yabawa gwamnatin jihar Bauchi bisa aiwatar da wadannan ayyuka gami da yadda gwamnatin ta inganta walwalar alkalai, sai kuma tasha alwashin ci gaba da aiki kafada da kafada da gwamnatin.

Shima da yake jawabi kwamishinan shari’ah kuma babban lauyan gwamnatin jihar Bauchi Barrister Yakubu Bello Kirfi ya bayyana cewa ma’aikatar ta samu kararraki 414 da suka shafi fashi, kisan kai, ayyukan ta’addanci gamida garkuwa da mutane da dai sauran su.

Ya kuma ce an magance guda 220 sai kuma 133 da ake kan gabatar da shari’ah akai da kuma guda 14 da suke jiran shari’ah.

Yakubu Bello Kirfi ya kara da cewa gwamnatin jihar Bauchi ta kuma yafe wa masu laifuka kimanin 106.

Leave a Reply