Uncategorized

Takaitattun labaran safiyar yau daga Baushe Times

DAGA IS’HAQ IDRIS GUIƁI

Assalanu Alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, goma sha bakwai ga watan Muharam, shekarar 1443 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da ashirin da shida ga watan Agusta, shekarar 2021.

  1. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce leƙa kwalejin horas da ƙananan hafsoshin soja NDA da ke Kaduna da kdinafas suka yi, ba za ta sa gwiwar sojoji ta yi sanyi ko kaɗan ba, a aniyar da suka dauka, ta ganin bayan waɗanda suka hana ƙasar nan sakat.
  2. Lucky Irabor babban hafsan tsaro, ya leƙa kwalejin ta NDA don tantance abin da ya auku da ɗaukar mataki.
  3. Hukumomin soja sun yunƙura, domin yin aiki tare da tsofaffin sojojin Nijeriya, don taimakawa magance matsalar tsaro da ke addabar ƙasar nan.
  4. Fadar Shugaban Ƙasa, ta zargi gwamnan jihar Binuwai Ortom da yin kalamai na iza wutar rikici na ƙabilanci da na addini. Fadar ta ce kullum kalamansa na haɗa faɗa ne tsakanin makiyayi da manomi, da kuma musulmi da kirista.
  5. A Talata mai zuwa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, zai ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi SUPER TUCANO guda 29 da aka auno, zuwa cikin jiragen mayaƙan saman.
    ƙasar nan a Abuja.
  6. ‘Yan Boko Haram da ‘Yan Ƙungiyar ISWAP na ta faɗa tsakaninsu da juna suna kashe juna a jihar Barno.
  7. Wasu bayanai na nuna cewa likitoci ‘yan Nijeriya, na ta ficewa daga ƙasar nan zuwa ci-rani ƙasashen ƙetare.
  8. A jihar Nasarawa an yi kidinafin wani sakataren hukumar zaɓe ta jihar.
  9. A jihar Binuwai wasu sun kashe mutum takwas, da kidinafin mutum guda.
  10. A jihar Filato, an kashe wajen mutum talatin da shida a Yelwan Zangwam. Har gwamnan jihar Lalong ya maido da dokar hana walwala ta sa’a 24 a Jos ta Arewa.
  11. A jihar Zamfara kidinafas da ‘yan fashin daji na ci gaba da cin karensu ba babbaka, har gwamnan jihar Matawalle, ya yi kiran a sa dokar ta ɓaci a Arewa ɓangaren tsaro.
  12. Hukumar kwastam na duba yiwuwar dawo da harajin kayan shaye-shaye na zaƙi da ake yi a nan cikin gida ba masu bugarwa ba.
  13. Ɗaliban jami’ar jihar Kaduna da na sauran manyan makarantun jihar da gwamnatin jihar ta ƙara wa kuɗin makaranta, na ci gaba sa faɗi-tashin neman kuɗin biya.
  14. Damina na ci gaba da kankama, masu wutar lantarki na ci gaba da ƙwauron wutar. Don yinin jiya zuwa yau da asubah, ba wutar babu dalilinta. Ko da aka kawo, ba ta daɗe ba suka ɗauke abarsu.
  15. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik na gwamnatin tarayya, na ci gaba da ƙorafin suna shirin cika shekara uku, suna dakon ariyas na sabon albashi.
  16. Wata ƙididdiga, na nuna Afirka ta Kudu ce ta yi wa ƙasashen duniya fintinƙau, wajen matsalar rashin aikin yi.

Is’haq Idris Guiɓi
Kaduna Nijeriya.

Leave a Reply