News

Gwamna Inuwa Ya Ƙaddamar Da Sabon Kamfanin Taki A Gombe

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zaƙulo damammakin da ke tattare da harkar noma a Jihar Gombe ta hanyar tallafawa masana’antun da suka jiɓinci harkar noma, waɗanda ya ce su na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙi da zamantakewa.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ƙaddamar da kamfanin sarrafa taki da sinadaran noma na Al-Yuma a garin Kwadon da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba.

Ya bayyana irin rawar da kamfanin zai taka wajen samar da ayyukan yi da kayan noma don bunƙasa samar da abinci da wadatarsa.

Ya bayyana ƙudurinsa na ci gaba da bunƙasa harkar noma a bisa ƙudurin sabunta fata na Shugaba Tinubu, musamman ƙudurinsa na bunƙasa noma don tabbatar da isasshen abinci a ƙasar nan.

“Kuma tun hawanmu kan karagar mulki a 2019, muke mayar da hankali kan samar da abinci. Domin mun yi imanin cewa ci gabanmu ya ta’allaka ne da noma,” in ji Gwamna Inuwa.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, akwai wadatacciyar ƙasa mai faɗin gaske a Gombe, ga kuma yawan al’ummar da sun kai su samar da wadataccen abinci, yana mai jaddada cewa, “Babu dalilin da zai sa Nijeriya ta dogara da shigo da abinci daga ƙasashen waje alhali muna da abin da za mu iya ciyar da kanmu”.

DCIM\100MEDIA\DJI_0399.JPG

Da ya ke yabawa da irin rawar da ‘yan kasuwa ke takawa wajen rage zaman banza, Gwamna Inuwa ya ce “Duk da cewa samar da ayyukan yi shi ne abu na farko da ya rataya a wuyan ‘yan kasuwa, aikin gwamnati shi ne ta samar da kyakkyawan yanayin haɓaka kasuwancin, don haka a shirye muke mu tallafawa duk wani dan kasuwa da ke son ya kafa kasuwancinsa a Jihar Gombe”.

Ya ce irin nasarorin da Gombe ta samu har sau biyu a fagen sauƙaƙa kasuwanci da kuma samun kyakkyawan matsayi har uku a fannin kyautata tattalin arziki da zamantakewa a matsayin shaida kan ƙudurin gwamnatinsa na samar da yanayi mai aminci don ‘yan kasuwa su ci gaba.

Gwamnan ya sanar da kawo karshen rabon tallafin abinci, maimakon hakan ya ce taki za a samar don ƙarfafa gwiwar jama’a su koma gona don magance matsalolin tattalin arziƙi.

Gwamna Inuwa ya sanar da sayan taki tan dubu 200 daga sabon kamfanin na Alyuma don rabawa manoman Jihar Gombe. “Za mu sayi taki don tallafa muku idan kun shirya komawa noma,” in ji shi.

Tun farko a jawabinsa na maraba, Shugaban Kamfanin taki da sinadaran na Al-Yuma, Alhaji Yusuf Ali Yusuf, wanda ya samu wakilcin Manajan Daraktan Kamfanin, Dakta Faruk Hamza, ya ce kyakkyawan yanayin kasuwanci da gwamnan ya samar a Jihar Gombe ne ya ƙarfafa musu kafa kamfanin a jihar.

Ya ce Gwamna Inuwa Yahaya ya samar da ingantattun manufofi tare da goyon baya daga gwamnatinsa ga ‘yan kasuwa.

Ya kuma yabawa Gwamna Inuwa bisa kishinsa ga noma, yana mai cewa kyawawan manufofinsa ne suka zaburar da su. “Kokarinka ya taimaka matuƙa wajen kawo wannan kamfani Jihar Gombe, kuma ga shi a ƙarshe aikin ya yi nasara,” in ji shi.

Ya ce kamfanin na da ƙarfin samar da tan dubu 120 na takin zamani kala-kala a duk shekara, “Har ila yau, muna samar da takin da zai dace da kowace irin ƙasa ko amfanin gona,” in ji shi.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Yamaltu Alhaji Abubakar Aliyu, ya godewa Gwamna Inuwa bisa samar da yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali don kafa irin waɗannan kamfanoni.

DCIM\100MEDIA\DJI_0394.JPG

Leave a Reply