Gwamnan Gombe Ya Ƙaddamar Da Biyan Diyyan Aikin Hanyoyin Tumfure Masu Tsawon Kilomita 11
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya ƙaddamar da biyan diyya ga masu kadarorin da aikin gina hanyoyin Tumfure zai shafa.
A yayin bikin, Gwamnan ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na inganta ababen more rayuwa da kyautata zamantakewa da tattalin arziƙin al’umma, inda ya kwatanta hakan da yadda gwamnatocin da suka shuɗe suka gaza samar da ababen more rayuwa ga yankin.
Ya ce tsawon hanyoyin zai kai kilomita 11, waɗanda za a shumfuɗa a arewaci da kudancin unguwar ta Tumfure, wanda wani ɓangare na aikin hanyoyi na Network 11-100.
Ya bayyana takaicinsa bisa gazawar gwamnatocin da suka gabata a jihar wajen samar da ababen more rayuwa ga unguwar, yana mai cewa yin aikin a wannan karo, shaida ce ta kawo ƙarshen mummunan shugabancin baya.
Duk da ƙalubalen da ke tattare da faɗuwar darajar Naira, Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kammala aikin hanyoyin na Tumfure a kan lokaci.
“Wannan aikin wani ɓangare ne na aikinmu na Network 11-100 da muke yi a wani ɓangare na Ƙaramar Hukumar Akko kuma tsawonsu ya kai kilomita 11 kamar yadda aka yi a wasu wurare da dama. Za a kammala waɗannan ayyuka ne cikin watanni tara, kuma mun riga mun gayyaci dan kwangila don fara aiki gadan-gadan da somin taɓin kaso 30 cikin 100 na jimillar kuɗaɗen don haka babu wani dalili na ƙorafi”.
Ya jaddada wajibcin da ke kansa na hidimtawa kowa ba tare da nuna son kai ko siyasa ba, yana mai bayyana buƙatar Nijeriya ta ɗauki kwararan sauye-sauyen tsara birane irin na ƙasashen da suka ci gaba.
“Dole ne mu koyi darasi daga tsare-tsare da dabarun raya ƙasa na wasu ƙasashe da suka ci gaba a faɗin duniya waɗanda suke aiwatar da sauye-sauyen tsara birane masu kyau saboda ƙwararan dokoki don tabbatar da ci gaban birane da garuruwa.”
Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma jaddada muhimmancin hukumomi irin su Hukumar Raya Birane ta Jihar Gombe (GOSUPDA) da hukumar zamanantar da harkokin filaye ta Gombe (GOGIS) wajen inganta tsare-tsaren birane da ingantaccen tsarin gudanar da harkokin filaye.
Ya kuma yi gargaɗi kan yadda ake yanka filaye ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ɗauki tsauraran matakai ta hannun hukumomin na GOSUPDA da GOGIS.
Gwamna Yahaya ya tunatar da jama’a cewa a matsayinta na mai kula da duk wassu harkokin filaye a jihar, gwamnati tana da ‘yancin kwace duk wani filin da aka sarrafa ba bisa ƙa’idar doka ba.
Gwamnan ya yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wasu harkokin filaye da ake yankawa ba bisa ƙa’ida ba, domin hukumomi irin su GOSUPDA da GOGIS doka ta ba su ikon yin maganin duk wani mai laifi komai girmansa.
Tun farko a jawabinsa na maraba, Shugaban kwamitin biyan diyyar, Malam Muhammadu Gambo Magaji, ya yabawa Gwamnan bisa himmatuwa da jajircewarsa wajen tabbatar da cewa al’ummar jihar sun samu hanyoyin zirga-zirga.
Gambo Magaji wadda shi ne kwamishinan kuɗi da bunƙasa tattalin arziƙi, ya yabawa gwamnan bisa ruɓanya yadda ake biyan diyya a jihar da kaso 100 bisa 100, yana mai cewa kwamitinsa zai tabbatar da adalci ga duk masu kadarorin da abin ya shafa.
Kwamishinan ya ba da sanarwar wa’adin makonni biyu da aka bai wa masu kadarorin da aka biya diyyan damar tattara kayayyakinsu don share fagen fara aiki gadan-gadan.
Shi ma da ya ke nasa jawabin, Kwamishinan Ayyuka da Sufuri Injiniya Usman Maijama’a Kallamu, ya gargaɗi masu kadarorin da aikin hanyoyin na Tumfure ya shafa su guji kutsawa filin da aka bari a gefen titi, yana mai cewa za a yi amfani da filin ne wajen sanya fitilun hanya da shimfida bututan ruwa.
Ya kuma miƙa godiya ga Gwamna Inuwa Yahaya bisa cika alkawarin da ya yi wa al’ummar Tumfure a lokacin yaƙin neman zaɓe, bayan shafe gwamman shekaru gwamnatocin baya basu cika musu irin wannan alkawarin ba.
Tun farko a jawabinsa, Shettiman Gombe kuma mai riƙon Hakimcin Gombe, ya jinjinawa Gwamna Inuwa Yahaya a inda wassu suka gaza, ya kuma yi ƙira ga al’ummar jihar su haɗa kai da hukumomi irinsu GOSUPDA da GOGIS don samar da kyawawan tsare-tsaren raya birane.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Akko da Hakimin Tumfure sun nuna matuƙar jin daɗinsu ga gwamnan kan aikin hanyoyin da sauran ɗimbin ayyukan raya ƙasa da yake yi wa yankin.