Ɗan Bindiga Bello Turji Ya Kwace Manyan Motocin Soja 2, Ya Kwashe Malamai
Hotunan bidiyo masu motsi sun karaɗe kafafen sadarwar zamani inda ke nuna ƙasurgumin ɗan fashin daji, Bello Turji da ‘yan tawagarsa su na murnar samun nasarar karɓe manyan motocin dakon kayan yaƙi na rundunar sojin Nigeriya guda biyu.
An kuma gano Turji da ‘yan tawagar nasa suna kwashe makamai da dama daga cikin motar sojojin da suka kwace.
Wani kwararren masanin tsaro da yaƙi da ‘yan ta’adda a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama shi ne ya tabbatar da faruwar wannan lamarin.
Makama ya ce sojoji sun samu wani rahoton haɗuwar da tawagar Bello Turji za su yi a wani sansaninsa.
A ƙoƙarin tawagar sojoji na kai samamen gaggawa a yankin bisa jagoranci wani matashin jami’in soja amma motar sojojin ta maƙale a cikin laka lamarin da ya hana su wucewa.
Makama ya ƙara da cewa a bisa wannan sojojin da ‘yan fashin dajin sun yi artabun wanda suka kashe wasu awannin suna ɓarin wuta kan juna.
“Bisa yanayin mamakon ruwan sama, iska bai kaɗawa a wannan ranar, hakan ya bai wa ‘yan bindigan damar ƙarfafa dakarun su.
“Sojoji sun yi yunƙurin amfani da ɗayan MRAP domin janyo wanda ya maƙale amma dukkaninsu sai suka maƙale cikin laka.”
Ya ƙara da cewa an samu ƙarin sojojin da suka sake zuwa domin taimakawa wajen janyo motocin MRAPS amma duk da hakan haƙa ba ta cimma ruwa ba.
“Don haka sojojin suka bar wajen tare da barin Motocin a wajen. Ba wani rauni ko asarar rai da aka samu a wannan artabun.
“Awanni baya, Turji da yaransa sun bayyana a wajen inda suka kama harbe-harbe sama tare da karɓe motocin sojojin.”
Rundunar soji dai har zuwa yanzu ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba.