Hausa

Gaskiyar Lamari Kan Wani Rubutu Mai Taken ‘Ku Daina Tutiya Da Aikin Cibiyar Masana’antu’

Daga Ismaila Uba Misilli

Wani rubutu na bata suna, kuma maras tushe balle makama ya jawo hankalin Gwamnatin Jihar Gombe a wani shafin sada zumunta na Facebook mallakin wani wai shi Bala Sani, wadda ke ikirarin wai aikin cibiyar masana’sntu ta Dadinkowa dake Jihar Gombe aiki ne na Gwamnatin Tarayya wadda zata yi karkashin shirinta na musamman na bunkasa tattalin arziki a shiyyoyin kasar nan.

Bai kamata ma mu damu da har sai mun maida martani kan wannar kirkirarriyar gurguwar fahimta ba, amma akwai bukatar mu fayyacewa Gombawa da sauran nagartattun ‘yan Najeriya gaskiyar yadda lamarin yake.

Aikin Cibiyar Masana’sntu ta Muhammadu Buhari, tunani ne wadda hazikin gwamnan mu mai hangen nesa Muhammadu Inuwa Yahaya ya faro, kuma ya fara bayyana batun ne lokacin da suka kai wata ziyarar aiki kasar Rasha tare da Mai Girma Shugaba Muhammadu Buhari a shekara ta 2019, inda ya ayyana kudurin nasa karara karon farko a bainar jama’a na kafa cibiyar masana’antun ta Muhammadu Buhari. Cibiya ce mai girman kadada dubu daya, wacce aka tsugunar a kusa da madatsar ruwa ta Dadinkowa kan babbar hanyar Gombe zuwa Biu.

Bayan bayyana wannan kuduri na gwamnan ne aka kaddamar da tawagar kwararru don duba yiwuwar kafa cibiyar, da binciken yanayin wurin kafa ta, dama tsara yadda aikin zai gudana. Bayan kammala aiki da mika rahoton su ga gwamnati, gwamnatin jihar ta biya masu filaye a wurin diyyar kadarorin su. Daga nan kuma gwamnatin ta tallata a jaridu, bukatar neman kamfanonin da za su yi ayyuka daban-daban a rukunin farko na aikin cibiyar.

Daga nan ne kuma aka mika sunayen kamfanonin da suka yi nasara ga majalisar zartaswa ta jiha. Bayan gamsuwar da majalisar ta yi ne kan yadda aka bi tsarin da duk ya kamata, ta amince da bada kwangilar ayyuka rukunin farko na cibiyar, kan kudi fiye da Naira biliyan 16 da miliyan 400, Kuma kamfanin bunkasa haraji na jihar wato GROCOL ne zai samar da kudaden aiwatar da aikin.

Yana da muhimmanci a sani, cewa gwamnatin jihar tana tattaunawa da Bankin Bunkasa Ci Gaban Afirka AfDB don samar da wani bangare na kudaden gudanar da aikin. Haka nan tattaunawa ta yi nisa da Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu ta Tarayya kan sanya cibiyar masana’antun ta zama mahada ta fitar da kayayyakin da aka samar zuwa kasashen waje.

Bisa wadannan bayanai, ya kamata duniya ta sani cewa, gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ba zata yi kasa a gwiwa ba kan wannan kuduri nata, kuma zata yi farin ciki da maraba da duk wani dan jihar wadda zai iya taimakawa wajen shigo da Gwamnatin Tarayya cikin lamarin, ko kuma ma jawo hankalin masu zuba jari zuwa jihar.

Dole ne a jinjinawa wannan hazikin Gwamna namu wadda ya lashe lambobin yabo na zama na daya a fannoni daban-daban, bisa yadda ya faro tare da kirkiro wannan kuduri na kafa cibiyar masana’antu irinta ta farko a yankin arewa maso gabas ba tare da wata gudunmowa ta kudi ko kayan aiki ba daga wata cibiya ko hukuma ta Gwamnatin Tarayya ko ta duniya.

Muna kara jaddada cewa, cibiyar masana’antu ta Muhammadu Buhari abu ne da Gwamna Inuwa Yahaya ya kirkira, kuma aiki ne na Gwamnatin Jihar Gombe ita kadai dari bisa dari.

Ya kamata Bala Sani da iyayen gidan sa da suka rasa makama, suka koma irin wannan yarfe da batanci na cewa wai aikin wannar cibiya wani bangare ne na aikin Gwamnatin Tarayya na musamman na habaka tattalin arziki a shiyyoyin kasar nan su gaggauta ganowa tare da shaida mana inda Gwamnatin Tarayyar take gina nata cibiyar, su kuma shaida mana inda aka kai kudaden da aka ware don wannan aikin, domin kuwa Gwamnatin Jihar Gombe bata da masaniya kan kudaden da aka ce an warewa wannar cibiya ta Gwamnatin Tarayya, ba a kuma bata wassu kudade masu kama da haka ba wai har Naira biliyan 3.

Mai ra’ayi:

Ismaila Uba Misilli,

Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan Jihar Gombe

Leave a Reply