Uncategorized

An amince da bukatar gina sabbin makarantun firamare guda hudu a mazabar chiroma


Daga: Mohammed kaka Misau, Bauchi
A kokarinsa na samar da wakilci na gari ga al’ummar mazabarsa da kuma wakilci na gari, Dan majalisa mai wakiltar mazabar chiroma a majalisar dokoki ta jiha kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar dokoki ta jiha Hon.Bakoji Aliyu Babbo, kudirin bukatar sa ta samar da isassun makarantu wa al’ummar mazabarsa ta samu amincewa.

Tun da farko Hon. Bakoji Aliyu Babbo ya gabatar da bukatar samar da makarantun firamare guda goma, ina da aka samu amincewa da guda shida.

A wannan karon kuma dan majalisar ya sake samu amincewa da ragowar guda hudun.

Sakataren hukumar ilimi ta karamar hukumar shine ya shaida hakan ga al’ummar yankin Marewo, tare da bada filin gonar sa dake yankin domin aiwatar da aikin ginin makarantar yankin.

Sakataren ya kuma basu tabbacin cewa da zarar an kammala aikin ginin dukkan makarantun, hukumar zata aike head master da zasu jagoranci makarantun ba tare da bata lokaci ba.

Yankunan da za’ gina musu makarantun sun ne,garin Marewo dake gundumar Kukadi, garin Rigar Busa a gundumar Ajili, garin Da’ako a gundumar Sirko da kuma garin Ganjin Gwando dake Gundumar Gugulin.

Leave a Reply