Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Goma sha Daya: Laduban Azumi na wajibi

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

Azumi yana da laduba masu yawa, wadanda Azumi ba ya cika sai da su. Kuma wadannan laduba kashi biyu ne:
1) Laduba wajibai, wadanda wajibi ne mai Azumi ya kiyaye su.
2) Laduba mustahabbai, wadanda ya kamata mai Azumi ya kiyaye su.

Daga cikin laduban Azumi na wajibi; ya wajaba a kan mai Azumi ya lazimci Ibadu na aiki da na magana, mafi muhimmancinsu shi ne Sallolin farilla, su ne mafi girma a cikin rukunnan Muslunci bayan Shahada guda biyu. Don haka wajibi ne mai Azumi ya kiyaye Sallolin farilla, ya kiyaye su da sharudansu da wajibansu, ya yi su a Masallaci a cikin jam’i, saboda hakan yana daga cikin aiyukan Taqwa, wadanda aka shar’anta Azumi, aka farlanta shi saboda su. Don haka rashin kiyaye Sallah a cikin Azumi yana kore Taqwa, kuma yana janyo wa mutum azabar Allah. Allah ya ce: {Sai wasu suka zo a bayansu, suka tozarta Sallah, suka bi abubuwan sha’awa, da sannu za su hadu da gayya (wani kwari a Jahannama). Sai dai wanda ya tuba ya yi imani, ya yi kyakkyawan aiki, wadannan su za su shiga Aljanna, kuma ba za a zalunci kowa ba} [Maryam: 59 – 50].
Akan samu wasu masu Azumi suna sakaci da Sallar Jam’i tare da wajabcinta a kansu. Saboda Allah ya yi umurni da yin Sallah ne a cikin jam’i, wannan ya sa hatta makaho maras jagora Annabi (saw) bai yi masa rangwamen rashin zuwa Sallar jam’i ba. Ya tabbata daga Abu Huraira (ra) ya ce: ((Wani mutum makaho ya zo wajen Annabi (saw) ya ce: Ya Manzon Allah, ba ni da jagora da zai kai ni Masallaci. Sai ya nemi Annabi (saw) ya yi masa rangwame, yana yin Sallah a gidansa, sai Annabi (saw) ya yi masa rangwame. Bayan ya juya ya tafi, sai ya kira shi, ya ce masa: “Shin kana jin kiran Sallah”? Sai ya ce: Eh. Sai ya ce: “To ka amsa”)). Muslim (653).

Rashin halartar Sallar farilla cikin jam’i yana sa mutum ya rasa falalar Sallar, Annabi (saw) ya ce: ((Sallar jam’i ta fi Sallar mutum daya da daraja ishirin da bakwai)) Bukhari (645), Muslim (649).

Kuma barin halartar jam’i sifa ce ta Munafukai, bayan zai janyo wa mutum azabar Allah, zai sa ya yi kama da Munafukai, kamar yadda ya tabbata daga Abu Huraira (ra): ((Sallah mafi nauyi ga Munafukai ita ce Sallar Isha’i da Sallar al-fijr, da a ce sun san abin da ke cikinsu na lada da sun zo musu ko da da rarrafe ne. Hakika na yi nufin na sa a yi Sallah, a tayar da Iqama, sai na umurci wani ya yi limanci, sai na tafi tare da wasu mutane, a tare da su akwai damin itace, zuwa ga mutanen da ba sa zuwa Sallar jam’i, don na kona musu gidajensu)). Bukhari (657), Muslim (651).
Saboda haka sakaci da Sallah, a cikin jam’i yana daga cikin munanan aiyuka da suke hana cikan ladar Azumi, mai sai mutum ya sha yunwa da kishirwan banza.

Daga cikin laduba na wajibi; wajibi ne mai Azumi ya nisanci dukkan abin da Allah da Manzonsa (saw) suka haramta na maganganu da aiyuka. Wajibi ne ya nisanci karya, wato ya fadi abin da ba a yi ba ya ce an yi, ko ya fadi abin da aka yi amma bisa sabanin yadda abin ya auku. Mafi girman karya kuma shi ne karya wa Allah da Manzonsa (saw), kamar mutum ya danganta ma Allah halasta wani abu, ko haramtawa ba tare da ilimi ba. Allah ya ce: {Kada ku fadi ga abin da harsunanku suke siffantawa na karya, wannan halal ne wannan kuma haram ne, alhali karya kuke yi ma Allah. Lallai wadanda suke kirkiran karya ma Allah ba za su rabauta ba. Jin dadi ne kadan, sai kuma azaba mai radadi} [al-Nahl: 116 – 117].
Ya tabbata daga Abu Huraira da waninsa (ra) Annabi (saw) ya ce: ((Duk wanda ya yi mini karya to ya tanadi wajen zamansa a gidan wuta)) Bukhari (110), Muslim (3).
Kuma ya tabbata Annabi (saw) ya ce: ((Ku nisanci karya, saboda karya tana shiryarwa ga fajirci, lallai fajirci kuma yana shiryarwa zuwa ga wuta. Mutum ba zai gushe ba yana karya, yana kirdadon yin karya face an rubuta shi a matsayin makaryaci a wajen Allah)).Bukhari (6094), Muslim (2607).

Haka wajibi ne ya nisanci cin naman mutane da gulmansu, ko da kuwa anbaton mutum da sifarsa wacce ba ya so a kira shi da ita ce, kamar a ce masa gurgu, makaho, kuturu ta fiskar aibantawa, ko abin da yake ki na halaye, kamar a kira shi da wawa, soko da sauransu. Saboda Annabi (saw) ya yi bayanin giba da cewa shi ne: ((Ambaton dan’uwanka da abin da yake ki. Sai aka ce masa: To idan ya kasance yana da wannan abin fa? Sai ya ce: idan yana da shi to ka ci namansa, idan kuma ba shi da shi to ka yi masa kage)). Muslim (2589).
Allah Madaukaki ya yi hani a kan giba, har ya siffanta shi da mummunan kama, ya nuna giba ya yi kama da cin naman mutum a zahiri bayan ya mutu. Allah ya ce: {Kar sashenku ya yi giban sashe, yanzu dayanku zai so ya ci naman dan’uwansa bayan ya mutu? To ku kyamace shi} [al-Hujraat: 12].

Haka kuma ya nisanci annamimanci da hada fada, da yin batanci a kan mutum, wannan shi ma yana cikin manyan laifuka. Annabi (saw) ya ce: ((Annamimi ba zai shiga Aljanna ba)) Bukhari (6056), Muslim (105).
Annamimnaci shi ne bata tsakanin mutane, da haifar da fitina a tsakaninsu, mutum ya dauki magana daga wannan ya kai ga wancan don ya bata tsakaninsu, ya haifar da gaba da kiyayya a tsakaninsu.

Haka wajibi ne mutum ya nisanci gisshu da cuta a cikin mu’amalar kasuwanci ko sana’a, saboda cuta yana daga cikin manyan laifuka, Annabi (saw) ya ce: ((Wanda ya yi mana gisshu ba ya tare da mu)) Muslim (102).
Gisshu shi ne cuta da yaudara da cin amana da rashin aminci a tsakanin mutane cikin mu’amala. Dukkan wanda cuta ya zama hanyar abincinsa to ya sani haramun yake ci, wuta yake ci a cikinsa, babu abin da zai kara masa sai nisa da Allah.

Haka kuma wajibi ne mai Azumi ya nisanci kayan kade-kade da raye-raye da kayayyakin wasanni, da sauran abubuwa da suke wannan layi, wadanda suke haramun ne, balle kuma a ce idan ya hadu da sauti mai haifar da fitina da motsa sha’awa. Shi ya sa Annabi (saw) ya hada su da zina, inda ya ce: ((Lallai wasu mutane za su kasance a cikin al’ummata, suna halasta zina da hariri, da giya da kayan kida da waka)). Bukhari (5590).

Duk wanda bai kiyaye wadannan laduba ba, bai nisanci wadannan munanan aiyuka ba, to ko shakka babu zai iya wayan gari ya yi kishirwan banza, da yunwan banza, kamar yadda Annabi (saw) ya ce: ((Duk wanda bai bar fadin karya da aiki da ita ba, da aikin jahilci to Allah ba ya bukatar ya bar cin abincinsa da abin shansa)). Bukhari (6057).
An ruwaito daga Jabir (ra) ya ce: (Idan kana Azumi to jinka ma ya yi Azumin, ganinka ya yi, harshenka ya yi, ya kame daga karya da aiyukan haramun. Ka nisanci cutar da makwabci, ka lazimci nitsuwa, kar Azuminka da shan ruwanka ya zama daidai).

Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu kishin al’umma da tausayin talakawa.

Leave a Reply