Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Goma sha Biyu: Laduban Azumi na Mustahabbi

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

Azumi yana da Sunnoni Mustahabbai, wadanda ya kamata mai Azumi ya kiyaye su, don ya samu cikakke lada a kan Azuminsa, daga cikinsu:

Yin Sahur yana daga cikin sunnonin Azumi, shi ne mutum ya ci abinci a karshen dare kafin al-fijr. Annabi (saw) ya yi umurni da haka inda ya ce: ((Ku yi sahur, saboda akwai albarka a cikin sahur)). Bukhari (1923), Muslim (1095).
Haka Annabi (saw) ya bayyana cewa; Sahur ne abin da ya raba Azumin Musulmai da na Ahlul Kitabi, inda ya ce: ((Banbancin Azuminmu da na Ahlul Kitabi shi ne cin abincin sahur)). Muslim (1096).
Don haka ake so mai Azumi ya yi sahur da duk abin da ya samu, ko da ruwa ne ko dabino.

Kuma yana daga cikin abin da ake so shi ne a jinkirta sahur din, ya kasance a kusa da ketowan alfijr. Shi ya sa Allah ya ce: {Ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana muku daga bakin zare} [al-Baqarah: 183].
Ma’ana har sai hasken al-fijr ya bayyana daga duhun dare.
Saboda haka ba gwaninta ba ne mutum ya ki yin sahur, har ya zo yana bugan kirjin cewa; shi ba ya yin sahur.

Daga cikin Mustahabban Azumi akwai gaggauta buda baki, da zaran an tabbatar da faduwar rana to sai a gaggauta yin buda baki, saboda Annabi (saw) ya ce: ((Mutane ba za su gushe suna tare da alheri ba matukar sun gaggauta buda baki)) Bukhari (1957), Muslim (1098).
An so mutum ya yi bude baki da zaran rana ta fadi, ko da da ruwa ne ko dabino. Ya tabbata daga Anas (ra) ya ce: ((Annabi (saw) ya kasance yana yin buda baki kafin ya yi Sallah, yana cin danyen dabino, idan bai samu danye ba sai ya yi da busasshen dabino, idan bai samu ba sai ya kurbi ruwa)). Abu Dawud (2356), Tirmiziy (696).

Kuma lokacin buda baki lokacin amsa addu’a ne, don haka ake so mutum ya yi kokari wajen yin addu’o’i da rokon Allah biyan bukatunsa na alheri. Annabi (saw) ya ce: ((Lallai mai Azumi yana da addu’a a lokacin buda bakinsa, wacce ba za a mayar da ita ba)). Ibnu Majah (1753).
Daga cikin addu’an da aka ruwaito daga Annabi (saw) akwai fadinsa: ((Zahaba al-zama’u, wabtallatil uruqu, wa thabata al-ajru insha Allah)). Abu Dawud (2357).
Ma’ana; kishirwa ya tafi, jijiyoyi sun jika, lada ya tabbata insha Allahu.

Daga cikin Sunnonin Azumi da ladubansa ana son yawaita karatun Alkur’ani da zikiri da addu’o’i da rokon Allah da Sallah da sadaka. Ya tabbata Annabi (saw) ya ce: ((Mutane uku ba a mayar da addu’arsu, mai Azumi har sai ya yi buda baki, adalin shugaba, addu’ar wanda aka zalunta, Allah zai daga ta a saman gajimare, sai a bude mata kofofin sama, sai Ubangiji ya ce: na rantse da girmana da buwayata zan taimake ka ko da bayan wani lokaci ne)) Tirmiziy (2526), Ibnu Majah (1752).
Kuma Annabi (saw) ya kasance mai yawan kyauta a Ramadhan, kamar yadda ya tabbata daga Ibnu Abbas (ra) ya ce:
((Annabi (saw) ya kasance ya fi kowa kyauta, kuma kyautansa ya fi yawa a Ramadhan, saboda Jibril ya kasance yana haduwa da shi a kowane dare a watan Ramadhan har ya kare, Manzon Allah (saw) yana karanta masa Alkur’ani, idan Jibril ya hadu da shi ya kasance mafi kyauta fiye da iska mai kadawa)). Bukhari (4997), Muslim (2308).

Daga cikin laduban Azumi ana so mai Azumi ya halarto da girman ni’imar Allah gare shi, ta yadda ya datar da shi ga yin Azumin, ya saukaka masa shi, kuma ya cika masa Azumin, saboda akwai mutane da yawa wadanda suka rasa wannar daman, imma saboda ajali ya riske su, ko rashin lafiya, ko gazawa, ko sun bata daga hanya, don haka mai Azumi ya gode ma Allah a kan ni’imar Azumi, wacce kofa ce ta samun alherai masu yawa, na samun falalan ibadu, da gafaran zunubai da daukakar daraja a gidan Aljanna.

Don haka bayi ku lazimci laduban Azumi don rabauta, ku nisanci sabuba masu tauye Azumi su hana samun ladansa, ko cikarsa.

Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu.

6 thoughts on “DARUSAN RAMADHAN

Leave a Reply