Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Goma sha Tara: ZAKKAR FIDDA KAI

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

Idan bayin Allah sun cika Azuminsu na watan Ramadhan Allah ya wajabta musu Zakkar Fidda Kai, wacce za a fitar a Ranar Eidi, don yawalta mabukata da abinci.

Zakkar fidda kai ibada ce da take da alaka da Azumin watan Ramadhan.
Da Larabci ana kiranta “Zakatul Fidir”. An kira ta da sunan Zakkah ne saboda tana gyara halin mutum, ta habaka shi, ta sanya shi cikin masu kyauta da karamci.

Sababin shar’anta ta shi ne shan ruwa daga Azumin Ramadhan.
Hikimar shar’anta ta ita ce don ta tsarkake mutum daga abubuwan da ya aikata na yasassun maganganu da na batsa a lokacin da yake Azumi. Ya tabbata daga Ibnu Abbas (ra) ya ce: ((Manzon Allah (saw) ya farlanta Zakkar fidda kai don tsarkake mai Azumi daga yasasshiyar magana, da magana ta batsa, kuma don samar da abinci ga miskinai)). Abu Dawud (1609), Ibnu Majah (1827).

Ita Zakkar Fidda kai tana rataye ne a wuyan mutum kansa, ba da dukiya take rataye ba. Shi ya sa aka wajabta ta a kan kowa, ba ta takaita kan masu dukiya kadai ba. Don haka ita wannar Zakka ta wajaba a kan kowane Musulmi, mace ko namiji, babba ko karami, da ko bawa. Saboda ya tabbata daga Ibnu Umar (ra) ya ce: ((Manzon Allah (saw) ya farlanta Zakkar fidda kai za a bayar da sa’i daya na dabino, ko sa’i na sha’er, wajibi ne a kan bawa da da, namiji da mace, karami da babba daga cikin Musulmai. Kuma ya yi umurni da a fitar da ita kafin mutane su fita Sallar Eidi)). Bukhari (1503), Muslim (984).

Zakkar tana wajaba a kan kowane Musulmi ne idan yana da sa’i daya da ya karu a kan abincinsa tare da iyalinsa na ranar Eidi da darensa. Haka kuma ko da rabin sa’i ne ya saura, to sai ya ciyar da shi, saboda Allah ya ce: {Ku ji tsoron Allah iya abin da za ku iya} [al-Tagabun: 16].

Kuma wannar Zakka tana wajaba a kan Musulmi ko da kuwa bai yi Azumi ba saboda wani uzuri, kamar wanda tsufa ya hana shi yin Azumin, ko mace mai jinin haifuwa, wacce tsawon wata gudan ba ta samu ta yi Azumi ko daya ba, ko yaro, ko da kuwa jariri ne. Saboda fadin Annabi (saw) a Hadisin Ibnu Umar (ra) wanda ya gabata: ((Karami da babba daga cikin Musulmai)). Bukhari (1503), Muslim (984).

Bashi ba ya hana fitar da Zakkar Fidda kai ta kowace fiska, saboda bashi yana rataye ne da Dukiya, amma ita Zakkar kuma tana rataye a wuyan mutum kansa.

Asali Zakkar ta wajaba a kan kowa ne da kansa, amma idan wani ya fitar ma wani bisa yardarsa, kamar mai gida ya fitar ma iyalansa, da ‘ya’yansa to ya wadatar. Saboda aikin Sahabbai ya tabbatar da haka, Nafi’u Maulan Ibnu Umar ya ce: ((Ibnu Umar ya kasance yana fitar da Zakkar ga yaro da babba, har ya kasance yana fitar ma ‘ya’yana)). Bukhari (1511).
Don haka wannan ya nuna cewa; yaran da ba su da dukiya fitar musu za a yi, haka aikin Sahabbai ya nuna.

Zakkar fidda kai tana wajaba ne da zaran rana ta fadi a ranar karshe na Ramadhan, in an shiga daren Eidi. Dalili a kan haka shi ne Hadisin Ibnu Umar (ra): ((Manzon Allah (saw) ya farlanta Zakkar fidda kai a kan mutane ga Ramadhan, za a bayar da sa’i daya na dabino, ko sa’i na sha’er, wajibi ne a kan da da bawa, namiji da mace daga cikin Musulmai)). Bukhari (1511), Muslim (984).
Fadinsa (saw) cewa: ga Ramadhan shi yake nuna da zaran Ramadhan ya zo karshe, rana ta fadi a yinin karshe na Ramadhan to Zakkar ta wajaba.

Bude baki daga Azumin Ramadhan yana tabbata ne da zaran Rana ta fadi an shiga daren Eidi. Wannan ya sa duk yaron da aka Haifa a daren Eidi, bayan faduwar rana to Zakkar ba ta wajaba a kansa ba, saboda bai riski Ramadhan ba. Amma da a ce za a haife shi kusa da faduwar rana, kafin a sha ruwa, to Zakkar ta wajaba a kansa.

Lokacin fitar da Zakkar shi ne ranar Eidi da safe, kafin a fita Masallacin Eidi. Saboda ya tabbata daga Ibnu Umar (ra) ya ce: ((Kuma Manzon Allah (saw) ya yi umurni da a fitar da ita kafin fitan mutane zuwa ga Sallar Eidi)). Bukhari (1503), Muslim (984).
Don haka wajibi ne Zakkar ta isa hanun Fakirin da za a ba shi Zakkar ko wakilinsa kafin a fita zuwa Masallacin Eidi.

Ya halasta a fitar da Zakkar kafin ranar Eidi da rana daya ko biyu, saboda Sahabbai sun aikata hakan, sun kasance suna bayar da ita kafin ranar Eidi da rana daya ko biyu. Nafi’u ya ce: ((Ibnu Umar (ra) ya kasance yana bayar da ita ga masu karbanta, kuma sun kasance suna bayarwa kafin ranar Sallar da kwana daya ko biyu)). Bukhari (1511).

Haramun ne fitar da ita bayan Sallar Eidi, kuma ba ta isarwa ga wanda ya fitar, saboda Hadisin Ibnu Umar wanda ya gabata, cewa; Annabi (saw) ya yi umurni da fitar da ita kafin fita Sallah. Da kuma Hadisin Ibnu Abbas (ra) ya ce: ((Manzon Allah (saw) ya farlanta Zakkar fidda kai don tsarkake mai Azumi daga yasasshiyar magana, da magana ta batsa, kuma don samar da abinci ga miskinai. Wanda ya bayar da ita kafin Sallah ta zama Zakka karbabbiya, wanda ya bayar da ita bayan Sallah ta zama sadaka daga cikin sadakoki)). Abu Dawud (1609), Ibnu Majah (1827).
Wannan Nassi ne a kan cewa; Zakkar ba za ta wadatar wa mutum ba idan ya bayar da ita bayan Sallar Eidi, kuma ba za a karbe ta a matsayin Zakkar Fidda kai ba, ta zama sadaka ce kamar sauran sadakoki.
Amma idan wani uzuri ne ya sa bai fitar a kan lokacinta da ba fa, misali ya yi tafiya, ya wakilta wani ya fitar a kan lokacinta, amma sai da ya dawo daga tafiyar sai ya samu mutumin bai fitar da ita a kan lokaci ba, to ba shi da laifi a wajen Allah, amma zai fitar da ita ko da kuwa bayan Eidin ne da kwanaki. Wannan kiyasi ne a kan rama Sallah ga wanda ya yi bacci ko ya manta ta.

Ya halasta mutum ya bayar da Zakkar ga Kungiyoyin Agaji masu rijista ko amintattu. Sai su zama wakilai ga su fakirai da za a ba su wannar Zakka. Saboda haka idan mutum ya bayar da Zakkar wa kungiyar a kan lokaci, amma ita kungiyar kuma ba ta raba ba har sai bayan ranar Eidin, to shi dai Zakkarsa ta yi. Ta yiwu su kuma wani uzuri ne ya hana su raba ta a safiyar ranar Eidin, ko kuma wata Maslaha ce ta sa suka jinkirta.

Wajibi ne a fitar da Sa’i guda na abinci, a kan kowane Musulmi. Saboda Hadisin Ibnu Umar (ra) ya ce: ((Manzon Allah (saw) ya farlanta Zakkar fidda kai za a bayar da sa’i daya na dabino, ko sa’i na sha’er, wajibi ne a kan bawa da da, namiji da mace, karami da babba daga cikin Musulmai. Kuma ya yi umurni da a fitar da ita kafin mutane su fita Sallar Eidi)). Bukhari (1503), Muslim (984).
Malamai sun yi ittifakin a kan cewa; Sa’in da ake nufi a nan shi ne Sa’in Annabi (saw). Ana kaddara shi a wannan zamani da kilo biyu da gram 40.

Abin da ya wajaba a fitar shi ne sa’i na irin abincin mutanen gari, kamar shinkafa, masara, gero, dawa da makamancinsu ko garinsu. Dalili a kan haka shi ne Hadisin Abu Sa’eed (ra) ya ce: ((Mun kasance a zamanin Manzon Allah (saw) muna fitar da sa’i na abinci a ranar Eidi. Ya ce: abincinmu ya kasance shi ne sha’er da zabib da cukui da dabino)). Bukhari (1510).
Don haka cewa da ya yi abinci, ya nuna jinsin abinci ne ya wajaba a fitar, ba dole sai nau’in abincin da aka ambata a cikin Hadisan ba, saboda su ne abinci a wancan lokacin. Don haka sai ambaton nasu ya zama tamkar misali ne, ba wai an ayyana su ba ne a matsayin dole su za a fitar. shi ya sa ya gabata a Hadisin Ibnu Abbas (ra) ya ce: ((Don samar da abinci ga miskinai)). Abu Dawud (1609), Ibnu Majah (1827).
Wannan ya sa Malamai suka ce; wajibi ne a fitar da abinci, ba kudin abincin ba.

Ana bayar da zakkar ce ga talakawa; Fakirai da Miskinai. Babu laifi a bayar da zakkar mutum goma ga Fakiri mutum daya, ko kuma a bayar da zakkar da ta fito daga bangare daya ga Fikirai goma a raba musu, saboda Annabi (saw) ya yi bayanin iyakacin abin da za a bayar din ne, wato sa’i daya, amma bai kayyade yawan wadanda za a ba su ko yawan abin da za a bai ma kowa daga cikinsu ba.

‘Yan’uwa ku yi kokari ku yi da’a ma Allaha a wannar Zakka, saboda farilla ce, Allah ya wajabta ta ne ta harshen Manzon Allah (saw).

Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya. Ya sa mun dace da daren Lailatul Qadr.
Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu tsoron Allah da kishin al’umma da tausayin talakawa.

Leave a Reply