Uncategorized

DARUSAN RAMADHAN

Dr. Aliyu Muhammad Sani Misau
Islamic University of Madinah, Madinah Saudi Arabia

Darasi na Goma sha Hudu: Abubuwan da suke karya Azumi

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar’anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma’aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari’a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

Akwai abubuwan da suke bata Azumi, su warware shi, allah Madaukakin Sarki ya ce: {Yanzu kam ku sadu da su (matanku), ku nemi abin da Allah ya rubuta muku, ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana muku daga bakin zare na al-fijr, sa’annan ku cika Azumin zuwa dare} [al-Baqarah: 183].
A cikin wannar Aya mai girma, Allah ya ambaci ginshikan abubuwan da suke warware Azumi, a Sunna kuma Annabi (saw) ya bayyana cikon sauran.

Abubuwan da suke warware Azumi nau’uka ne guda bakwai:
Na farko: Jima’i:
Shi ne saduwa da mace ta hanyar saka zakari cikin farji. Wannan shi ne mafi girman abubuwan da suke warware Azumi, kuma shi ya fi girman zunubi. Duk lokacin da mai Azumi ya sadu da mace to Azuminsa ya baci, sawa’un Azumin farilla ne ko na nafila. Idan da rana ne a watan Ramadhan, kuma Azumin wajibi ne a kansa, to wajibi ne sai ya rama, kuma sai ya yi kaffara mai tsanani, ita ce: ‘yanta baiwa mumina, idan kuma bai samu ba, to sai ya yi Azumi wata biyu a jere, ba zai sha ko daya ba sai da uzuri na Shari’a, kamar ranakun Eidi, da ranakun Tashreeq (ranakun 11, 12, 13 ga Zul-hijja), ko wani uzuri na zahiri, kamar rashin lafiya ko tafiya ba don yin dabara ma Shari’a ba. Idan ya sha rana daya ba tare da uzuri ba, to dole zai sake tun daga farko, don dole ne sai an samu jerantawa.
Idan kuma ba zai iya yin Azumin ba, to sai ya ciyar da miskinai sittin, kowane miskini zai ba shi rabin kilo da gram goma na abinci, shinkafa ko masara d.s.
Ya tabbata wani mutum ya sadu da matarsa da rana a watan Ramadhan, sai ya tambayi Annabi (saw) a kan haka, sai ya ce: ((“Shin za ka samu baiwa”? Ya ce: A’a. “Shin za ka iya Azumi wata biyu (a jere)”? Ya ce: A’a. Ya ce: “To ka ciyar da miskinai sittin”)). Bukhari (6821), Muslim (1111).

Na biyu: Fitowan maniyyi:
Idan mutum ya fitar da maniyyi daga gare shi da gangan, imma saboda sunbantar mace, ko shafan jikinta, ko ta wata hanyar daban, ta hanyar sha’awa to Azuminsa ya warware. Saboda wannan yana cikin sha’awar da hakikanin Azumi ba ya tabbata sai da nisantarsa. Annabi ya ce: ((Zai bar abincinsa da abin shansa da biyan sha’awarsa don ni)). Sahihul Bukhari (7492), Sahihu Muslim (1151).
Amma sunbantar mace da shafan jikinta ba tare da maniyyi ya fito ba, ba ya karya Azumi, saboda abin da ya tabbata daga A’isha (ra): ((Annabi (saw) ya kasance yana sunbantan iyalinsa, yana runguma alhali yana Azumi, amma ya kasance ya fi ku rike sha’awarsa)). Bukhari (1927), Muslim (1106).
Ya tabbata Umar bn Abi Salamah: ((ya tambayi Manzon Allah (saw): Shin mai Azumi zai sunbaci iyalinsa? Sai Manzon Allah (saw) ya ce masa: “Tambayi wannar”, yana nufin Ummu Salamah, sai ta ba shi labarin cewa; Manzon Allah (saw) ya kasance yana aikata hakan. Sai ya ce: Ya Manzon Allah, ai kai Allah ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubanka da na gaba, Sai Annabi (saw) ya ce: “Na rantse da Allah na fi ku taqwa da tsoron Allah”)). Muslim (1108).
Don haka idan mai Azumi yana jin tsoron idan ya yi sunbantan zai fitar da maniyya, ko har hakan zai ja shi ga saduwa da iyalin, saboda ba zai iya rike sha’awarsa ba, to a nan haramun ne a kansa ya yi sunbantan, a babin “sadduz zari’a”, wato toshe kofar barna, da kuma kare Azuminsa daga baci.

Amma fitar da maniyyi saboda mafarki, ko tunani ba tare da aiki ba, ba ya karya Azumi, saboda na mafarki ba ya cikin zabin mutum, na tunani kuma Allah ya yi afuwa a kansa. Annabi (saw) ya ce: ((Allah ya yafe ma al’ummata abin da ta raya a ranta matukar ba ta yi aiki da shi ko ta furta a magana ba)). Bukhari (5269), Muslim (127).

Na uku: Cin abinci ko shan abin sha:
Shi ne shigar da abinci ko abin sha zuwa ciki, ta hanyar baki ko hanci, na dukkan nau’ukan abin ci ko sha. Saboda fadin Allah: {Ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana muku daga bakin zare} [al-Baqarah: 183].
Duri ta hanci shi ma kamar ci da sha ta baki ne, shi ya sa ya tabbata Annabi (saw) ya ce: ((Ka shaqa ruwa a hanci sosai, sai dai idan ka kasance mai Azumi)). Abu Dawud (2366), Tirmiziy (788), Nasa’iy (87), Ibnu Majah (407).
Amma shanshana wari ko kamshi ba ya karya Azumi.

Na hudu: Abin da yake da ma’anar ci da sha:
Misali karin jini, ko karin ruwa. Idan aka yi wa mutum karin jini ko na ruwa to Azuminsa ya karye, saboda jini shi ne abin da abinci yake samarwa a jikin mutum, haka karin ruwa, shi kuma yana madadin abinci ne, duk da cewa; mutum ba abinci ya ci a zahiri ba. Don haka za su dauki hukuncin ci da sha.

Amma allura ta magani, ba ta karin ruwa ba, ba ta warware Azumi, ko da kuwa mutum ya ji dandano ko dacinta a makokwaronsa. Ita allura ba ta warware Azumi, saboda ba a madadin abinci da abin sha take ba, don haka ba za ta dauki hukuncin cin abinci ba.

Na biyar: Yin kaho:
Fitar da jini ta hanyar kaho yana karya Azumi, saboda fadin Annabi (saw): ((Mai yin kahon (wanzami) da wanda ake masa kahon duka Azuminsu ya karye)). Abu Dawud (2367), Tirmiziy (774), Ibnu Majah (1679).
Da wannan Malamai suke ganin jan jini mai yawa a jikin mutum, wanda zai yi tasiri a jikin mutum, shi ma yana karya Azumi, sai dai idan ya zama larura, to wajibi ne ya karya Azumin nasa, daga baya sai ya rama.
Amma fitar da jini saboda habo, ko tari, ko basir, ko ciwon rauni, ko cire hakori, jan jini kadan don yi test, ko fitan jini saboda soka allura, duka ba sa karya Azumi, saboda ba kaho ba ne, kuma ba sa tasiri a jiki kamar yadda kaho yake yi.

Na shida: Amai da gangan:
Shi ne fitar da abin da ke cikin mutum na abinci ko abin sha ta hanyar baki. Saboda Annabi (saw) ya ce: ((Duk wanda amai ya rinjaye shi babu ramuko a kansa, amma wanda ya nemo aman da gangan, to dole ya rama Azumin)). Abu Dawud (2380), Tirmiziy (720), Ibnu Majah (1676).
Don haka duk wanda ya janyo amai da gangan, to Azuminsa ya karye. Amma idan ba da gangan ba ne to Azuminsa bai karye ba.

Na bakwai: Fitowan jinin haila ko biki:
Fitowan jinin haila ko biki daga mace yana karya mata Azumi, saboda fadin Annabi (saw) game da mace: ((Shin ba tana barin Sallah da Azumi ba idan tana jinin haila?)). Bukhari (304) Muslim (79).
Don haka duk lokacin da mace ta ga jini ya zo mata, na haila ko na biki to Azuminta ya baci, sawa’un a farkon yini ne ko a karshensa, ko da kuwa kafin faduwar rana ne da minti daya. Amma idan bai fara fitowa ba, har sai da rana ta fadi, to Azumin nata ya inganta.

Wadannan su ne abubuwan da suke karya Azumi. Saboda haka haramun ne mai Azumi ya yi daya daga cikin wadannan abubuwa, matukar Azumin nasa na wajibi ne, kamar Azumin Ramadhan, ko na kaffara, ko na bakance, sai dai idan akwai uzuri na Shari’a da zai halasta masa hakan, kamar tafiya ko rashin lafiya da makamancinsu. Saboda duk wanda ya fara aiki na wajibi to dole ya karasa shi, ya cika shi, sai dai idan da uzuri.
Sa’annan duk wanda ya yi daya daga wadannan abubuwa a tsakiyar rana a watan Ramadhan, ba tare da uzuri ba, to dole ya yi kama baki, har rana ta fadi, don kiyaye alfarman watan, kuma ramuko ya wajaba a kansa. Amma idan akwai uzuri to ramuko ne kawai ya wajaba a kansa.
Amma idan Azumin nafila ne, to ba dole sai ya cika shi ba, ko da babu uzuri kuwa, amma ko shakka babu abin da ya fi shi ne cikawan.

Ya ku ‘yan’uwa, lallai wajibi ne mu kiyaye aiyukan da’a, mu nisanci aiyukan sabon Allah, mu yi ibada ma Allah, mu girmama wajibansa, kar mu yi wasa da su, mu sani abin da mutum zai yi na ibada a halin rayuwarsa shi zai amfane shi a Duniya da Lahira, musamman a ranar Lahira, ranar da mutum zai yi nadaman lokacinsa da ya bata a Duniya ba tare da aikin da’a ma Allah da neman lada ba. Mu ribaci wannar ganima a rayuwarmu kafin wucewar lokacinta; wannan wata mai albarka, da ma rayuwar gaba daya lokaci ne na kasuwanci da Allah da neman riba, kar mu yi sakaci, kar mu gafala, duk wanda ya yi sakaci zai yi hasara, kuma zai yi nadama a lokacin da ba za ta yi amfani ba.

Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da yawaita aiyukan da’a a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya. Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu tsoron Allah da kishin al’umma da tausayin talakawa.

Leave a Reply