Uncategorized

June 12 Bai Dace Da Ranar Dimukradiyya Ba

Daga Najib Sani

Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2018 lokacin yana yakin neman tazarce ya aiyana 12 ga watan June na ko wani shekara a matsayin ranar dimokradiyyah a maimakon 29 ga watan mayu. Hakika shugaban kasa yana da hurumin ware ko wace rana a matsayin ranar hutu a kasa.

Saidai kuma a tunani na, June 12 ba itace tafi dacewa da ranar dimokradiyyah ba saboda ba wata hujja mai karfi da zai sa June 12 ya zamo ranar tunawa da dimokradiyyah a Nigeria saboda dalilai masu zuwa a kasa.

A gani na, May 29 ita tafi dacewa fiye da ko wace ranar a matsayin ranar dimokradiyyah. Da farko idan muka dubi tarihin zabukan Najeriya daga 1923 zuwa yau, zamu ga cewa zaben 1999 zuwa yau shi akafi samun nasara.

Misali, zaben 1923 wanda shine na farko a Najeriya bai ba wa yan kasa cikakken dama ba saboda yan majalisu ne kawai aka ba wa yan kasa damar zaba yayinda masu mulkin mallaka suke shugabancin gwamnatin tarayya.

Sa’annan kuma yan shekara 21 zuwa sama wadanda suke iya mallakar kudi a kalla £100 a shekarar data gabaci zabe sune kadai aka basu damar kada kuri’a.

Kazalika, wadanda aka yanke musu hukuncin kisa, ko zaman kurkuku na fiye da shekara guda, ko masu tabin hankali duk an haramta musu zabe a lokacin.

Su kan su yan majalisun da aka zaba, shugaban mulkin mallaka na lokacin Clifford ya nada mutane 13 cikin yan majalisu a matsayin yan majalisa baya daga zababbun.

Daga cikin su akwai wakilan yan kasuwa, jami’an banki, masu tonan ma’adanai da masu jiragen ruwa.

Ya nada wasu kuma su wakilci jihohi da ake cewa cibiyoyin kasuwanci ne kamar su Calabar, Kano, Lagos da Port Harcourt.

Zaben da aka sake yi bayan wancan shine na 1959 lokacin samun yancin kasa wanda ake ce wa jamhuriya ta farko. Anyi zaben ranar 12 ga Disamba 1959. Saidai an samu juyin mulki daga sojoji shekara shida kacal bayan kafa gwamnatin farar hulan kuma ba a sake zabe ba sai 1979 lokacin da Shagari ya kayar da Awolowo. Duk zabubbukan jumhuriya ta farko da ta biyu zabubbuka ne da aka gudanar bisa kabilanci. Jam’iyyun lokacin suma duk suna wakiltar bangarori ne (Ma’ana sashi sashi) a madadin su zamto Jam’iyyun kasa. Don haka suma jumhuriya na farko da na biyu basu chanchanci zama ranar tunawa da dimokradiyyah ba.

Ranar 6 ga watan Augusta 1983, an sake yin zabe yadda Shagari ya zarce amma bai dade ba janar Muhammadu Buhari ya masa juyin mulki.

Tun daga lokacin sojoji ne suka ta mulkan Najeriya har shekarar 1993 lokacin da janar Ibrahim Babangida ya yanke shawarin mika mulki wa farin hula da ya fahimci tsarin dimokradiyyah yana cigaba da samun karbuwa a mafi yawan kasashen duniya.

Shi wannan zaben an gudanar dashi ne ranar 12 ga watan June tsakanin Moshood Abiola da Bashir Tofa. Abiola shine ake ikrarin ya lashe zaben yanda ya samu kuri’u miliyan takwas da wani abu yayinda Bashir Tofa ya samu kuri’u miliyan biyar da wani abu. Saidai kafin a sanar da wanda ya lashe zaben, Babangida ya soke zaben bisa wasu dalilai nashi.

Al’amarin da ya janyo cecekuce da zanga zanga musamman a garuruwan yarbawa. Da yaji wuta sosai Babangida daga baya ya nada Shonekam daga yankin da Abiola ya fito don kwantar da hankalin kasa. Amma duk da mika mulki da Babangida yayi wa Bayarbe lokacin bai sa yayi farin jini a gun yan uwan mu yarbawa ba don har yanzu suna sukarsa don soke zabe mai inganci.

Kash! Kafin gwamnatin riko da Babangida ya nada don ta sake shirya sabon zabe sai ga janar Sani Abacha yazo ya kifar da gwamnatin kuma yayi ta mulki har 1998 lokacin da wasu da har yau ba a san su waye bane suka kashe shi.

Daga nan ne dimokradiyyah ta samu damar da bata taba samu ba a Najeriya bayan janar Abdulsalam Abubakar da ya maye gurbin Abacha ya shirya ingantacciyar zabe da ya kawo Olusegun Obasanjo a matsayin sabon shugaban farar hula bayan ya kayar da Olu Falae.

Tun lokacin dimokradiyyah ta samu gindin zama a kasar nan yau shekara 22 a jere ba tare da sojoji sunyi juyin mulki ba. An rantsar da shi ne ranar 29 ga mayu 1999 tare da gwamnoni 36.

Bisa wadannan dalilai nake cewa ranar 29 ga mayu ita tafi chanchanta a ringa tunawa a matsayin ranar dimokradiyyah a maimakon June 12 a Najeriya.

Karin hujjojin sune; sabanin zabubbukan 1959, 1979, 1993 da aka soke ko aka gudanar bisa turban kabilanci, bangaranci, rikice rikice ko kuma juyin mulki daga sojoji, zaben 1999 yafi nuna hadin kai tsakanin yan Najeriya.

Alal misali, Obasanjo yayi takara ne da dan uwansa Bayarbe kuma wanda suka fito daga yanki daya wato Olu Falae. Obasanjo dan jihar Ogun ne shi kuwa Falae daga Ondo yake.

Abu na gaba, Obasanjo bai bawa yan Najeriya kunya ba lokacin mulkinsa domin yayi kokari wajen daura kasar a turban cigaba ya kuma samar da tsaro da hada kan yan Najeriya da kafa hukumomin yaki da rashawa.

Bugu da kari, zaben June 12 1993 ba shine na farko ba a Najeriya, ba shi bane wanda yafi ko wanne zaman lafiya, ba shi bane kuma wanda ya daure ba. Toh ta yaya ya zamo ranar dimokradiyyah a Najeriya? Maganar da nake yi shine May 29 ita tafi dacewa da ranar dimokradiyyah tunda ita ce ta daure yanda farar hula suke mika mulki wa farar hula wajen shekara 22 yanzu.

Ku huta lafiya!

Ra’ayin Malam Najib Sani