Uncategorized

Yadda ‘Yan Shi’a Suka Jagoranci Jerin Gwanon Nuna Goyon Bayan Falastinawa A Bauchi

Sheikh Yashi yayin da ke jagorantar Jerin gwanon

Daga Khalid Idris Doya 

A Juma’ar nan ne dubban jama’a suka fito kan titi inda suka zagaye gari da nufin nuna goyon bayansu ga al’umman Palastinu wanda Yahudawa ke zalumta kamar yanda masu gangamin suka bayyana.

Muzaharar wacce aka faruta daga makarantar Fudiyya da ke unguwar Shagari ta nausa titin kofar Fada tare da mikewa zuwa titin Kobi ta nausa Wuniti tare da Shan kwana ta nausa titin Tashan Babiye kana ta sake daukan saiti zuwa titin Kofa Ran hade da shan kwana ta nausa Baba Sidi tare da kitse hancinta a massallacin Juma’a na Baba Ajiya da ke tsakiyar garin.

Malam  Ahmad Yusuf Yashi, wakilin ‘yan uwa musulmai almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky na jihar Bauchi ne ya jagoranci masu zagayen garin, ya bayyana cewar sun fito ne domin amsa kiran Ayyatullahi Imam Khumaini na kiran illahirin jama’a da suke amfani da ranar Juma’ar karshen ramadana wajen tunawa da raunanan Palasdinawa da kuma sauran wadanda ake zalumta a fadin duniya.

Ya kuma kara da cewa a irin wannan ranar su na kuma tuna da kuma yin dubiya kan halin da sauran jama’an duniya ke ciki musamman wadanda ake zalumta.

A cewar Ahmad Yashi sun fito ne domin su goyi bayan al’ummar Falastinu tare da tir da zalumcin da Yahudawa ke yi wa al’ummar Falastinuwa, ya nuna cewa shirin Yahudawa ba ga zallar Falastinuwa ya tsaya ba so suke su mamaye yankin Gabas ta tsakiya baki daya.

Ya ce: “Wannan fitowa da muke yi ba ma ga zallar Falastinuwa ba ne, a gaskiyar magana don dukkanin musulman duniya da raunanan da suke rayuwa a doron kasa. Domin da Isra’ila za ta yi nasara kawar da wadanda suke Palastinu to za ta mamaye dukkanin Gabas ta Tsakiya ne, wadannan kasashen irinsu Lebonon, Siriya, Jordan, Yusra da makamantansu. Domin ta taba gwada wannan yunkurin nata a 1967 na mamaye sassan wadannan wuraren.

“Su na nan suna da wannan tunanin da wannan burin. A takaice ma har sun bai wa shirinsu suna da cewa za su samar da Isra’ila babba wanda sun ce za su hada har da Madina daman sun ce Madina kasarsu ce, Annabi da ya zo ne ya koresu a nan.

“Don haka ya kamata musulmai su shiga cikin hayyacinsu ba magana ce ta ‘yan Shi’a ko ‘yan kaza ba. A’a lamari ne da ya shafi musulman duniya baki daya da duk kuma wanda yake da rauni a doron kasa. Kiranmu a nan shi ne al’umma ta zo da Sunnanta da Shi’anta a fito a yi Allah wadai da abun da Yahudawa ke yi a wannan yankin da kuma nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu. Kuma insha Allahu nasara na nan tafe ga al’ummar Falastinu,” ya tabbatar.

“Wannan fitowar tamu amsa kira ne na Imam Khumaini domin mu nuna goyon bayanmu ga raunanan Palasdinawa wadanda Yahudawa ke zalumta a kowani lokaci. Sannan kuma muna sake jadda cewar dole ne massallacin Qudus ya dawo hanun musulmai. 

“Shi wannan massalacin na Quds shi ne masallaci na uku a daraja amma an wayi gari yana qarqashin ikon Yahudawan Sahayoniya kuma wajibi ne mu kwato wannan massalacin domin na musulmai ne,” a cewarsa.

Wakilinmu da ya kasance da muzaharar ya shaida mana cewar masu muzaharar sun yi ta waken bayyana halin da al’ummar Falasdinawa ke ciki, da kuma nuna goyon bayansu a garesu. A gefe guda kuma suna nanatawa, gami da jaddawa kan cewar sai an kwato massalacin nan na Al-Aqsa daga hanun azzaluman Yahudawan Sahayoyi. 

Mun jiyo masu muzaharar na cewa “Massallacin Kudus namu ne, kwatoshi ya zama wajibi- Mutuwa a kan Isra’ila-Mutuwa akan Amurka-Mu Bamu xaukan zilla”. Da dai sauran wakokin nuna goyon baya da kuma makasudin fitar nasu.

An dai yi gangamin na nuna goyon bayan Falastinu a Bauchi lafiya, a wajen rushe jawabin an kona tutar kasar Amurka da na Isra’ila a yayin gangamin.

An yi zagayen lafiya a cikin garin na Bauchi.


Leave a Reply