Uncategorized

Shugabannin Matasan PDP Na Misau Sun Ziyarci Hon. Bobbo Don Mika Godiya Wa Gwamna

Daga: Mohammed kaka Misau, Bauchi.

Shugabannin Matasan jam’iyyar PDP na gundumomi 16 da ke karamar hukumar Misau sun ziyarci shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Bauchi, Hon. Baboji Aliyu Bobbo domin miki godiyarsu wa gwamnan Jihar Bala Muhammad bisa kyautukan motoci da Mashina da ya yi wa al’umman yankin a makon jiya.

Da ya ke jawabin lale a garesu, Hon. Bobbo ya nuna gayar farin cikinsa bisa ziyarar tare da jawo hankalinsu da su cigaba da bada nasu gudunmawar domin cigaban Gwamnatin Bala Muhammad.

Ya ce, Kaura na da shirye-shirye da daman gaske da yake son aiwatarwa domin kyautata rayuwar Mata da matasa a Jihar.

Ya basu tabbacin samun goyon bayan gwamnati a kowani lokaci domin samar wa al’umman yankin da jiha baki daya cigaba mai ma’ana.

Leave a Reply