Uncategorized

Shaikh Zakzaky Ya Yi Tir Da Wulakanta Alkur’ani A Sweden

  • Ya Bulaci A Hukunta Wadanda Suka Aikata Hakan

Daga Khalid Idris Doya

Sheikh Ibraheem Yakub Zakzaky, jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Allah-wadai da yadda wasu mutane suka wulakanta Alkur’ani mai girma a kasar Sweden.

Ya nuna abun da ya faru a matsayin cin fuskar addinin musulunci sai ya yi kira ga masu fafutukar ‘yanci a fadin duniyar nan da su fito su yi tir da wannan aika-aikar.

Sheikh Zakzaky ya yi kiran ne ta cikin wani bayani da ofishinsa ya wallafa a shafin Facebook a ranar Asabar 1 ga Yulin 2023, inda ya ce tabbas abin da ya faru labari ne marar dadi, kuma hakan ya raunata zuciyar al’ummar Musulmai da masu neman ‘yanci a duniya.

Shehin Malamin Shi’a din ya misalta abin da ya faru da cin fuska ga Musulunci da Musulmi, sai ya nemi dukkanin masu neman ‘yanci a duniya da ka da su yi shiru kan lamarin nan.

Ya kuma ce dole ne a hukunta wadanda suka aikata hakan domin a fadinsa Alkur’ani Mai Girma ba abun wasa ba ne.

Zakzaky ya ce, “Wannan labari mara dadi na cin zarafin Alkur’ani mai girma a kasar Sweden, ya raunata zukatan dukkanin musulmi da masu neman ‘yanci na duniya.”

“Tabbas kona Alkur’ani mai tsarki ba wai cin fuska ne ga Musulunci da musulmi ba, cin fuska ne ma ga dukkanin addinan duniya da mabiyansu. Don haka, ya zama wajibi ga duk wani mai ‘yanci da kada ya yi shiru akan wannan aiki”.

“Mun yi Allah wadai da wannan mummunan aiki da wadanda suka aikata shi kuma muna kira da a gaggauta hukunta su,” a cewar sakon shehin Malamin.

Leave a Reply