Uncategorized

Tazarce: Bala Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Bauchi

Daga Khalid Idris Doya

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad kuma dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin lemar PDP, ya samu nasarar sake zama gwamnan Jihar bayan zaben da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben da karfe 10:34am na ranar Lahadi, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, mukaddashin shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, ya shaida cewar Bala Muhammad ya samu nasarar sake zama gwamnan Jihar Bauchi ne da kuri’u 525,280 da ya kayar da babban abokin nemansa na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar da ya samu kuri’u 432,272.

Sannan, shi kuma dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar NNPP, Sanata Halliru Dauda Jika ya samu kuri’u 6,496 a yayin zaben da aka gudanar.

Abdulkarim ya shaida cewar a yayin zaben gwamnan jihar na Bauchi, adadin masu zabe 2,7492,68 ne a jihar Bauchi, kuma an tantance masu jefa kuri’a 1,058,381 inda kuma adadin kuri’u 1,034,379 ne suka kasance masu kyau, kana an soke kuri’u guda 15,221.

Ya kara da cewa, adadin kuri’u 1,049,600 ne aka kada a yayin zaben na gwamnan jihar Bauchi da ya gudana ranar 18 ga watan Maris na 2023.

Farfesa Abdulkarim ya ce, bayan gamsuwa da dukkanin matakan doka na lashe zabe da kuma samun rinjayen, don haka ne ya ayyana Bala Muhammad a matsayin gwamnan Jihar Bauchi da ya samu nasara.

Idan za a iya tunawa dai ayarin wasu fitattun mutane a jihar Bauchi ne suka yi gayya a karkashin tawagar Air Marshal Sadique Baba Abubakar da nufin su sauya Bala daga kujerar mulki, sai dai bukatar tasu ta gamu da cikas.

Daga cikin wadannan fitattun mutanen akwai tsohon Kakakin Majalisar Dokokin tarayya, Yakubu Dogara, Dattijo Bello Kirfi, tsohon gwamna Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, dan majalisar wakilai Mai Wakiltar mazabar Bauchi cikin gari, Yakubu Shehu da sauransu amma dukkanin su Bala Muhammad ya samu nasara a kansu.

Wakilinmu ya nakalto cewa, ‘yan takara sha hudu daga jam’iyyun siyasa daban-daban ne suka shiga aka dama da su a yayin zaben gwamnan jihar Bauchi, sai dai Bala Muhammad ya lallasa dukkaninsu.

Bala Muhammad dai ya samu nasarar lashe kananan hukumomi guda 15 da suka ha da Jama’are; Kirfi; Bogoro; Warji; Itas Gadau; Shira; Zaki; Ganjuwa; Dass; Alkaleri; Ningi; da Tafawa Balewa, sauran su ne Toro, Bauchi gami da karamar hukumar Dambam.

Yayin da shi kuma dan takarar gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar APC, Air Marshal ya samu nasara a kananan hukumomi biyar da suka hada da Giade; Gamawa; Darazo; Misau da karamar hukumar Katagum.

7 thoughts on “Tazarce: Bala Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Bauchi

Leave a Reply