Hausa

Bidiyon Mai Dafa Abinci Da Wani Ya Yaudara: Gwamnan Bauchi Ya Biya Sama Da Miliyan 7.5 Wa A’isha Ibrahim

Daga Khalid Idris Doya

Biyo bayan faifaiyin bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta a ranar Labara, wanda ke nuna wata mata dillaliyar dafa abinci da ke jihar Bauchi ta na kuka domin neman ɗauki da agajin gaggawa sakamakon yaudararta da wani mutumin da ya sa ta dafa abinci na sama da mutum 3,000 inda ta neme shi sama da kasa ta rasa.

A bidiyon, matar ta nuna fargabar cewa muddin ba a yi amfani da kayan abincin ba zai iya ɓaci saboda an riga an dafa komai kamar yadda suka yi da mutumin.

Kwamishinan Ma’aikatar Jin Ƙai ta jihar Bauchi, Hon. Hajara Yakubu Wanka ta sanya wa hannu da kanta, ta ce, bayan samun labarin lamarin, nan take gwamnan jihar Bala Muhammad ya umarceta da ta kai sauƙin gaggawa ga matar.

“Lamarin ya janyo hankalin mai girma Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad inda a nan take ya umarci ma’aikatar jin kai a ƙarƙashin ni da mu bi lamarin tare da taimaka ma wannan mata mai dafa abinci. Lamarin ya kaimu ga biyan naira miliyan bakwai da dubu ɗari biyar da goma sha shida (N7,516,000) na kuɗaɗen da ita mai dafa abincin ta kashe wajen haɗa abincin biyo bayan bincike da aka gudanar.”

Ita dai dillaliyar dafa abinci Aisha Ibrahim mai kamfanin dafa abinci ta ‘Northern Varieties Restaurant Bauchi’ ta yi bidiyo da aka yaɗa a shafin yanar gizo inda take bayanin cewa, sun yi yarjejeniya da wani mutum Babajide Aiyegbusi, jami’in sashin mulki na wata lungiya mai zaman kanta Malaria Consortium, kan ta samar musu da kayan abinci da suka haɗa da na karin kulumlo (tea break) da abincin rana da za su ciyar da mahalarta taron horaswa kan wayar da kai na kwanaki uku da ke gudana a ƙananan hukumomi Bauchi, Alkaleri da Kirfi, inda daga bisani ta neme shi sama da lasa ta rasa tare da kiran wayarsa sau adadin da sama baya ɗauka, kuma an nemi shi a ofishin sa baya nan.

A bidiyon ta na kuka tana nuna jerin kayan abincin da ta dafa inda ta fito ɓalo-ɓalo ta nemi tallafi da agajin masu hannu da shuni a arewa da su taimaketa su sayi abincin tare da yin sadaka da shi domin gudun kada abincin ya ɓaci ta tafka babban asarar domin cewarta mutumin ya sanyata ta ciyo bashin mutane wajen haɗa kayan abincin.

Wanka ta ƙara da cewa, “A bisa jin ƙansa da tausayinsa, nan take mai girma gwamna ya umarci ma’aikatata da mu gaggauta biyanta kuɗin da ta kashe wajen dafa abincin kuma mu raba abincin ga mabuƙata musamman a asibitoci, gidajen marayu da marasa galihu da sauran masu buƙata a cikin garin Bauchi.”

“Don cika wannan umarnin na gwamna, nan take ni da ma’aikatan ofis ɗina muka bi hanyoyin da suka dace wajen binciken nawa ta kashe da hakan ya kai mun biyata Naira miliyan 7,516,000 na kudaden da ta kashe da sauran wahalar hidimar dafe-dafe.”

A cewar ita mai dafa abincin jami’an tsaro na kan gudanar da bincike, don haka Kwamishinan ta ce, wannan ba shi ne irinsa na farko da ke faruwa a jihar Bauchi ba, “Ina kira ga masu sanya a musa abinci da masu dafawa da suke cimma yarjejeniyar da suka dace da bin matakan da suka dace kafin fara dafa abinci domin gudun asara.”

“Ina kira da a samu ƙarin wayar da kai da sadarwa mai inganci daga wajen dukkanin hukumomin gwamnati, sarakuna, kafafen sadarwa domin wayar wa mutane kai, kan muhimman hanyoyin da suka dace kowani ɓangare yake bi kafin fara aikin dafa abinci domin guje wa faruwar irin wannan lamarin a nan gaba. Masu dafa abinci suna buƙatar a kara wayar musu da kai domin gudun tafka asara.”

Leave a Reply