Hausa

Jinjina Da Yabo: Rayuwa Mai Albarka, Yayin Da Gwamna Inuwa Ya Cika Shekaru 60 Da Haihuwa

Daga Ismaila Uba Misilli

A ranar 9 ga watan Oktoba Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya (Dan Majen Gombe) ya cika shekaru 60 cif-cif da haihuwa. Abu ne mai ma’ana idan muka bibiyi rayuwar wannan dan talikin gwamna abin so ga kowa, bisa la’akari da ra’ayin shahararriyar masaniyar nan Laura Catherine Schlessinger game da dabi’un kwarai da nagarta, inda take cewa “Mutane masu nagarta sune ke fada su cika. Yayin da wasun su kuma ke bigewa da bada uzurorin ba gaira ba dalili.”

Kan wannan batu, muna magana ne takamaimai game da Mai Girma Gwamna, tun yana dan kasuwa zuwa dan siyasa ya zuwa hadimin al’umma, yayin da yake cika shekaru 60 a duniya, tuni ya hada duk dabi’un nagarta da kima, inda kyakkyawan jagoranci da hangen nesansa suka bayyana karara a ‘yan shekarun daya shafe yana jagorantar Jihar Gombe.

A fagen kasuwanci da aikin gwamnatin da ya yi, mun ga yadda ya yi fice da zama mutum mai nagarta, kima da sanin ya kamata, wadda ba ruwansa da nuna banbanci duk da cewa ya taso ne cikin gata da alfarma. Tun yana dalibi a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya zuwa lokacin aikin sa na gwamnati har kawo yau, ba abinda ya sa a gaba face hidimar al’umma, abinda ke alamta akidar nahiyar Afirkan nan ta ‘ubuntu’, wacce ke nufin yin komai don ci gaban al’umma.

Tabbas, wadannan muhimman batutuwa ne musamman a fagen siyasa, inda dabi’ar son rai ke cin karenta babu babbaka. Kawo yanzu dai Gwamna Inuwa ya ciri tuta, inda ya nusantar da mu yadda ya kamata “buri” ya kasance jigon aniyar mu ta hidimtawa al’umma a fagen aikin gwamnati bisa kyawawan manufofi. Wato dai batun nagarta.

Irin wannar sadaukarwa ce a matsayin sa na jigon al’umma ta sa wannan jinjina da yabo ta zamanto dole mu yi ta, musamman in muka dubi salon jagorancin sa ga Jihar Gombe wadda ba shi da wata makúsá, yayin da muke taya shi wannar murna a irin wannan muhimmin lokaci.

Ba sai an fada ba cewa jama’ar Jihar Gombe sun sanya buri da fata da yawa akan sa lokacin da aka zabe shi gwamna a shekarar 2019, musamman saboda nagartar sa da aka gani na ayyukan kwarai da ya yi a baya lokacin da ya rike mukamin kwamishinan kudin da bunkasa tattalin arziki a zamanin tsohon Gwamna Goje. A yau, alamu suna nuni da cewa kyakkyawar fatan da jama’ar jihar ke da shi akan sa da har ta kai ga sun kawo shi kan karaga sai ci gaba take yi da habaka saboda kyakkyawan jagorancin sa abun misali.

Manyan nasarorin da gwamnatin sa ta samu suna nuni da hankoron sa na gina sabuwar Jihar Gombe mai cike da damammaki, ta hanyar sauya tsarin tattalin arziki da zamantakewa dama na siyasar al’ummar jihar ta hanyar kyakkyawan shugabancin da yake baiwa kowa dama da ci gaba.

Komai yana tafiya yadda aka tsara, duk da cewa mun fuskanci babbar matsalar koma bayan tattalin arziki, wadda ke bukatan jajircewa da sadaukarwa. Hakanan himma da azama suna da matukar muhimmanci, wadanda in ba tare dasu ba, da ba a cimma wani abun kirki ba, kuma duk hakan na faruwa ne yayin da muke fuskantar adawa daga jam’iyyun hamayya. Na gamsu cewa kawo sauyi ba abu ne mai sauki ba, amma ta hanyar gaskiya da yin komai a bayyane, jama’a da kansu sun fahimci cewa Gwamna Inuwa alheri yake nufi wa Jihar Gombe da kyautata rayuwar al’ummar ta, kamar yadda hakan ta tabbata daga akidar nan tasa ta sanya “Gombe a farko”.

A yau, bisa hazaka da jajircewar sa, yanzu Jihar Gombe ce tayi fintinkau a fagen saukaka harkokin kasuwanci a Nijeriya, kuma jihar da aka yi amannan tafi kowace a yankin arewa maso gabas ta fuskar zaman lafiya.

Gwamna Inuwa Yahaya da tawagarsa suna aiki tukuru don faɗaɗa ci gaba a duk faɗin jihar cikin shekaru masu zuwa, yayin da gwamnati ke ƙara himma kan manufofin ci gaban data tsara tare da ɗaurawa kan nasarorin da aka samu a baya a fannonin more rayuwa da ilimi da kiwon lafiya da noma da tsaron rayuka da dukiyoyi bisa tsarin daftarin cimma muradun da aka sanya a gaba.

Wannan ɗan taliki yana hanƙoro ne na ganin Jihar Gombe ta yi zarra ta hanyar adalci da haɗin gwiwa da sassa daban-daban na cikin gida dana waje, yana aiki bil hakki da gaskiya kuma babu gazawa. A bayyane yake game da halin tausayi da gwamnan ke da shi wajen gudanar da mulki da kuma irin matakan da yake dauka wajen tabbatar da rage talauci. Jagorancin gwamna mai nagarta da riƙon amana ya canza rayuwar mu na gama-gari, don kuwa a cikin kankanin lokaci, ya yi abubuwa da ake ganin ba zai yiwu ba a baya.

Kyakkyawar fata yanzu ita ce tabbatarwa mutanen mu kyakkyawar gobe. Iko da jagoranci da hangen nesan sa sun sake fasalin al’amuran mu, yanzu muna zaune akan babbar shimfida na abin da jihar Gombe za ta iya kasancewa idan muka gamsu da kanmu kuma muka yi abubuwan da suka dace tare da bin tsarin ci gaban da aka sa a gaba.

Saboda haka, ina da tabbacin cewa duk wandanda ke bibiyan harkokin ilimi da kulawar lafiya da bunƙasa ababen more rayuwa da aikin gona da tallafi a jihar za su yarda da abubuwan dake faruwa a yanzu.

Ina ganin zamu fi iya danganta ci gaban mu da irin jajircewar gwamnan idan muka yi la’akari da shigo da babban jari a manyan fannonin bunkasa walwala da tattalin arzikin Jihar Gombe a nan gaba. Bisa ga dukkan alamu, shekaru masu zuwa na gaba zasu taho da karin ingantacciyar rayuwa ga jama’a. Wannan shine tasiri da muhimmancin kasancewar gwamnati da kwatanta kyakkyawan jagoranci a matsayin sa na madugun canji. Bisa wannar mahangar, a bayyane take cewa gwamnatin Inuwa Yahaya tana kokarin gina sabuwar Jihar Gombe ne da bunkasa ci gaban ta.

Tuni al’ummar mu suka yaba da kokarin tsame yara daga kan tituna da magance masu ficewa daga makaranta, don su koma su ci gaba da karatun su, musamman ganin yadda ilimin yara mata keda matuƙar muhimmanci wanda kuma dukkansu kyauta ne. Jama’a suna kuma godiya da ginin makarantu da kyautata makarantun kwana da kayan aikin su da maida hankali kan gina hanyoyi da dama ta hanyar shirin sa na gina hanyoyi kilomita 100-100 a kowace karamar hukuma, cikin kananan hukumomi 11 da muke dasu don bunƙasa tattalin arziƙi da fannin noma da raya kasa da samar da kayan aikin asibitoci daban-daban da sake farfado da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko a duk faɗin jihar, da samar da ruwan sha ga kowa, da ƙarfafawa mutanen mu gwiwa a harkokin kasuwanci tare kuma da aniyar kafa sansanin masana’antu na Gombe wanda a ƙarshe zai jawo hankalin kamfanoni da yawa waɗanda zasu samar da dubban ayyukan yi. Makomar Jihar Gombe tana da kyau sosai kuma jama’a sun yi imani cewa gwamnatin Inuwa Yahaya tana yin kyawawan ayyuka a jihar.

Hakika Jihar Gombe tana samun ci gaba a matsayin abin alfahari kuma zuciyar yankin Arewa Maso Gabas da kuma kasancewa abar alfahari ga ƙasa baki ɗaya, duba da rawar da take takawa wajen samar da ɗimbin ci gaban tattalin arziƙi da wadata mafi girma ga mutanen yankin da Najeriya baki daya. Don haka cika alkawura shine a gaban sa maimakon bayar da uzuri. Ya kasance abun misali. Ya kuma samu nasarori daban-daban a ayyukan sa na gwamnati, kuma akwai saura masu zuwa nan gaba. Babu shakka, Gwamna Inuwa Yahaya ya sanya mu muna alfahari da sabuwar rayuwar da muka samu kan mu a ciki. Kuma muna lura da hanyoyin da yake bi wajen samun nasaran gudanar da mulki a jihar. Salon jagorancir sa da fahimtar shugabanci sun taimaka wajen samun nasarori, kuma na yi imanin cewa ya cancanci yabo daga dukkannin mu musamman a wannan lokaci wanda a zahiri muke ganin ci gaba. Barkan mu da sake ganin zagayowar ranar haihuwar jajirtaccen jagora, Dan Majen Gombe!

Ismaila Uba Misilli, shine Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

12 thoughts on “Jinjina Da Yabo: Rayuwa Mai Albarka, Yayin Da Gwamna Inuwa Ya Cika Shekaru 60 Da Haihuwa

Leave a Reply