Uncategorized

Burina Kafin Na Bar Duniya

Banda fatar Allah ya mun gafara da kuma ya dayyaba zuriyata, babban abinda zan so in gani kafin in bar duniya shi ne na maimaita tuka mota cikin tsakiyar dare daga Zariya zuwa Argungu kamar yadda na yi a 1990 cikin tsanaki ba tare da tsoron komi ba don tsabar dawowar zaman lafiya a Nijeriya.

Na yi alkawari, in haka ya tabbata, zan wuce kogin Argungu in kwankwadi ruwansa, in yi alwala in yi nafilar godiya ga Ubangiji, in ci damun kifi, sannan in tuko mota in dawo Bauchi.

Hakika mu da muka san Nijeriya lokacin da take cikin tsaro rayuwar yau tana ba mu takaici, tunanin wace irin rayuwa za mu bar wa sauran yan Nijeriya a baya yana razana mu. Amma a kullum cike muke da fatar Allah ya kawo mana karshen wadannan musibu baki daya.

Zariya – Argungu

A shekara uku da na zauna a Zariya lokacin PhD dina, na kan yi kabu-kabu da motata, Peugeot Station Wagon, a cikin garin Zariya don in samu abin tumfayawa kan albashina na N1,000 a wata a matsayina na malami a Jami’ar Usumanu Danfodio, Sokoto. Kullum bayan magariba sai in yi sallama da iyalina a Shika in kamo hanya ina daukan fasinja zuwa Samaru, Hanwa, Aviation, Zaria Hotel, PZ, Sabongari, Kongo, Gaskiya, Wusasa da Zaria City, har zuwa a tashi sinima a Sabongari, mu gama kai mutane wadannan unguwanni sannan na kama hanyar Samaru in koma gida Shika wajen karfe 11 zuwa 12 na dare. A lokacin nakan hada har N100 a dare guda in na samu fasinja. In yi ta murna.

Ina cikin haka ne watarana wajen karfe 10 na dare, sai na ga wasu a gefen hanya kusa da Total dake PZ. Na tambaye su inda za su je. Suka ce mun za su je NYSC camp ne a Argungu. Suna neman mota. A wannan daren? Suka, E. Na ce zan kai su. Na mance nawa suka biya ni. Na shiga Total na cika tanki bayan na dauke su, na kama hanya. Na tsaya a Shika na yi sallama da iyali. Muka sunkuya. Tafiya muke, muna ta hira, har dare ya yi nisa, duk garuruwa sun yi tsit. Hanya kuma ba kowa sai mu da k’ugin motarmu kake ji da kuma manyan motoci kalilan bayan tafiya mai tsawo. Na tsaya a Miyanci na kara mai a wajen masu bumburutu.

Mun isa Sokoto wajen karfe 2.30am. Muka dau hanyar Argungu. Tafiya muke har muka isa ana kiran sallar fari, gab da asuba. Ba abinda ya same mu banda salansar motar da ta tsage, wacce na gyara da safe kafin in dawo. Na rika kalen fasinja a hankali har na dawo gida Zariya da wajen N300 a aljihuna, ina murna.

Har yau wannan tafiya tana raina. Na sha tafiya Sokoto da magariba ko da asuba ni da abokan aikina da muke karatu a Zariya a lokacin. Amma wannan tafiyar zuwa Argungu ita na fi tunawa. Kuma a duk gararambar da na rika yi irin wannan da mota a Arewa, ban taba gamuwa da komi ba ko tsoron komi ba don kyawon tsaro.

Abuja-Sokoto-Yola-Jos

Akwai tafiya makamanciyar wannan lokacin da a 2010 (?) maigidana NSA Ali Gusau ya aike ni wajen Sultan da Lamidon Adamawa da Gbon Gwom Jos yayin da aka kai harin ramuwar gayya na Dogo Na Hauwa. A tafiyata Sokoto har na bata hanya na bi ta Kaura na kewaya na bullo to Goronyo. Ba wata damuwa. Kashe gari na bar Sokoto da karfe 6 na safe na isa Yola da dare na ga Lamido da karfe 8 na dare. Na baro Yola da safe na iso na ga Gbonn Gwom da karfe 4 na yamma tare da marigayi Alh. Saleh Bayari, muka shirya mitin na farko tsakanin shugabannin Berom da na Fulani a fadarsa cikin garin Jos don tattaunawa da zaman lafiya.

Umuahia – Tambawal

Haka a 1983 bayan na gama NYSC kuma an ba ni aiki a NRCRI, na baro Umuahia da magariba da wani dalibina Abubakar Danfuloti Tambawal don zuwa Sokoto in kama aiki a Jami’a, cikin motarsa FIAT Climatizatta. Duk daren tafiya muke. Kashe gari muka bar Kaduna da yamma muka doshi Tambuwal muka isa da asuba lami lafiya.

Godiya da Fargaba

Mu kam rayuwarmu a Nijeriya a wancan lokacin alhamdulillahi. Eh, akwai rashin wadata tunda kunga ina cikakken malamin jami’a har ban iya ci da iyalina da biyan bukatuna da kyau kan albashina—wanda bai wuce N11,000 ba jimilla a shekara—amma a bar ka ka zauna lafiya da dabararka ma wani babban gata ne. Allah mun gode maka.

Amma na baya muke tunani. Yau ga wadannan wurare da na sani kamar cikin gidan gadonmu suna cikin halin ha’ula’I, wasu an tarwatse su, jama’a sun watse, wasu an k’one, wasu an gudu an barsu, kowa a kan hanya tsoro yake za a kama shi a yi garkuwa da shi ko yaushe, ga zaman kabilanci da gaba, ga rashin Imani, abin ba iyaka kuma ba dadin tunawa.

Addu’a

Ba abinda za mu yi sai kowa ya shiga addu’a Allah ya dawo mana da zaman lafiya. Kowa ya ji dadi yadda muka ji a baya. Duk masu hannu a wannan ta’asar Allah ka shiryar mana da su kamar yadda muke fatar ka shiryar da zuriyarmu, ka yalwata kowa, ka sanya zukatanmu, mu zauna tare cikin yarda da rikon amana da taimaka wa juna.

Buri Na karshe

Babban burina ba tarin dukiya ba ne, wanda alhmadulillahi Allah ya ba ni daidai gwargwado bayan gwagwarmaya ta shekaru. A’a. Burina in ga zaman lafiya ya dawo. Da hakan zai samu a rayuwata, da zan so in maimaita barin Zariya cikin dare in tafi har Argungu, in yi shukura, in bar duniya cikin kyakkyawan zato ga al’ummata. Wannan shi ne babban burina a yau. Kuma burin ba ba zai cika ba sai dukkanmu mun tashi da addu’a da aiki don zaman lafiyar. Hatta magana ta kasance wacce za ta taimaka wa zaman lafiya ce ba ta lalata al’amari ba da jawo rabuwar kanuwa ba.

Ga buri ga shekaru sun tafi. Abinda ya rage ba yawa. Allah ka nuna mun ranar…

Dr. Aliyu U. Tilde
1 June 2022

4 thoughts on “Burina Kafin Na Bar Duniya

Leave a Reply