Uncategorized

Da Dumi-Dumi: Gwamna El-Rufai Ya Warware Rawanin Sarakuna 2

Daga Idris Khalid 

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya amince da sauke rawanin Sarakunan gargajiya na Piriga da na Arak, Mai martaba, Jonathan Paragua Zamuna, da Mai martaba, Janar Aliyu Iliyah Yammah (rtd), bi-da-bi.

Wannan matakin dai na zuwa ne kwanaki bakwai da karewar wa’adin shugabancin gwamna Nasiru.

A wata sanarwar da kwamishiniyar kananan hukumomi na jihar, Hajiya Umma Ahmad, ta fitar a ranar Litinin da yammaci, ta ce, Sarakunan biyu za su daina gudanar da harkokin ofishinsu ne daga ranar Litinin 22 ga watan Mayun 2023. 

Kwamishiniyar ta ce an warware rawanin Sarakunan ne bayan shawarar da ma’aikatar kula da harkokin kananan hukumomi ta bayar bisa dogara da sashin 11 na dokar Masarautun gargajiya mai lamba 21 ta shekarar 2021. 

Kan hakan ta kara da cewa, “Babban Hakimin Garun Kurama, Babangida Sule shi ne zai kula da harkokin babbar Masarautar Piriga har zuwa lokacin da za a sanar da nada sabon Sarkin, kazalika, an umarci sakataren Masarautar da ya fara shirye-shiryen nada sabon babban sarkin.

“Gomna Ahmadu, sakataren Masarautar Arak shi ne zai kula da harkokin Masarautar kuma shi ne zai shirya nada sabon babban sarkin.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnati ta ga yadda martanin da Janar Iliyah Yammah ya bayar game da batun nadin hakimai hudu, sabanin wanda aka amince da shi a masarautarsa, da rashin zama a masarautar Arak.

“Warware rawanin Jonathan Zamuna kuma ya biyo bayan rikicin kabilanci da ya barke tsakanin al’ummar Gure da Kitimi na Piriga a karamar hukumar Lere, da rashin zama a cikin masarautar.”

Leave a Reply